1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta zargi sojin Najeriya da laifin kisan 'yan shi'a

Ramatu Garba Baba
November 2, 2018

Rundunar sojin Najeriya ta kare kanta daga laifin tauye hakkin dan adam da kungiyar Amnesty ta yi kan sojojin da suka dauki matakin anfani da karfi a magance rikicin da 'yan Shi'a sama da arba'in suka halaka.

https://p.dw.com/p/37ZOQ
Nigeria Schiitische Pilger in Kano
Hoto: Getty Images/AFP/A. Abubakar

Rundunar sojin Najeriya ta mayar da martani inda ta karyata zargin tare da wallafa wani hoton bidiyo na shugaban kasar Amirka ashafinta na twitter, a cikin bidiyon an ga Shugaba Trump ya na cewa, sojojin kasar Amirka na da izinin harbin duk wani dan gudun hijira da ya kuskura ya jefa musu duwatsu, Trump dai na magana ne kan rundunar da ke aikin hana kwararan bakin haure cikin Amirka. Sai dai a na ta sakon, rundunar sojin Najeriya ta bi hoton bidiyon na Trump da wani dan gajeren sako da ke cewa 'Kalli ka yi naka nazarin''

Kakakin ma'aikatar tsaron kasar John Agim a na sa bangaren, ya ce sakon martani ne ga masu sukar jami'an tsaro a matakin da suka dauka kan 'yan mazhabar Shi'a a artabun da Amnesty ta ce an rasa rayuka akalla arba'in da biyar. Amnesty da wasu kungiyoyi masu rajin kare hakkin dan adam sun soki matakin jami'an tsaro wajen anfani da karfin da ya wuce kima kan masu tattakin, wanda suka ce ya sabawa dokokin kasa. 'Yan mazhabar Shi'a sun gudanar da tattakin da ya rikide zuwa munmunar rikici ne, a kira da suke na son ganin an sako jagoransu Sheikh Ibrahim Zakzaky da ke tsare tun daga shekarar 2015.