Najeriya: Rikicin siyasa da canji sheka | Zamantakewa | DW | 28.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Najeriya: Rikicin siyasa da canji sheka

Wutar rikicin shugabanci na dada ruruwa a manyan jam'iyyun siyasar Najeriya tare da haddasa canjin shekar wasu 'yan siyasar daga wannan jam'iyya zuwa waccan.

A Najeriya a daidai lokacin da ya kasa da shekara daya da rabi a gudanar da zabe, guguwar neman gabaci ta taso a cikin jam'iyyun siyasar kasar na APC mai mulki da PDP mai adawa. A yayin da a Kano rikicin cikin gida ya kaure a jam'iyya mai mulki ta APC tsakanin 'yan Kwankwasiya da 'yan Gandujiya, tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma jigo a jam'iyyar APC, Atiku Abubakar ya canza sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin