Najeriya: PDP na zargin INEC da yin magudi | Labarai | DW | 26.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: PDP na zargin INEC da yin magudi

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi hukumar INEC da bayyana sakamakon da ya bambanta da sakamakon da ke hannunsu. Jam'iyyar ta ce alkaluman "ba daidai ba ne" kuma "ba za su aminta da su ba."

A daidai lokacin da hukumar zaben Najeriya INEC ke ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa, dan takarar jam'iyyar APC kuma Shugaba mai ci Muhammadu Buhari na kan gaba da yawan kuri'u a jihohi bakwai, yayin da Atiku Abubakar na babbar jam'iyyar adawa ta PDP ke binsa da yawan kuri'u a jihohi biyar.

Hukumar INEC ba ta yi martani kan matakin jam'iyyar PDP ba, amma tun da farko shugaban hukumar Mahmud Yakubu ya ce hukumar ba za ta iya daukar mataki kan korafin sakamakon jihohin da ba a gabatar a gabanta ba.

Masu sa ido kan zaben daga kasashen waje sun ce dage zaben da aka yi na mako guda ya rage tasirin zabukan a idanun duniya. Sai dai wasu kungiyoyi a Najeriyar na jan hankalin 'yan kasar kan muhimmancin zaman lafiya bayan sanar da sakamako.