Najeriya na tattaunawa da Avengers | Labarai | DW | 22.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya na tattaunawa da Avengers

Shugaban Tarrayar Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da cewar gwamnatinsa ta soma tattaunwa da tsagerun NDA na Yankin Niger Delta .

A cikin wata sanarwa da ya bayyana shugaban ya ce gwamnatin tana tattaunawa da 'yan Kungiyar Avengers na Yanki Niger Delta ta hanyar kamfanonin mai da ke a kudancin kasar.

Kungiyoyin tsagerun na Avengers sune ke da alhakin kai hare-hare a kan kamfanonin da ke yin aikin hako man fetir din a yankin Kudacin Najeriya a kan bukatunsu na ganin an yi adalci wajen raraba kudaden man da ake samu ga yanki, wanda ke fuskantar gurbatar muhali a sakamakon aikin na hakon man fetir.