Najeriya na son yin afuwa ga masu halin bera | Siyasa | DW | 29.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya na son yin afuwa ga masu halin bera

Wani kudurin da ke gaban majalisar wakilan Najeriya ya tanadi yafe wa mutanen da suka saci kudin kasa laifinsu muddin suka dawo da shi. Sai dai wannan mataki na shan suka duk da kudin da zai shigar aljuhun gwamnati.

 kiraye-kirayen yafe wa mutanen da suka nuna halin bera a kan dukiyar gwamnati da aka basu amana, lamari ne da aka dade ana batunsa a Najeriya a matsayin hanyar samun kudade ga gwamnati da ta dade tana koken an wawashe baitil-malin kasar.

Abin da ya kai ga majalisar wakilan Najeriya ta saurari kuduri na bukatar hakan da dan majalisa Hon Linus Okorie da ke wakiltar jam'iyyar PDP ya yi kan cewa ya hango kyakkyawar manufa da ma amfanin yin haka bisa halin da Najeriya ke ciki.

Sai dai tuni wannan yunkuri ya sanya tada jijiyar wuya a kasar musamman a tsakanin masu yaki da cin hanci da rashawa. Comrade Nasiru Kabir na kungiyar kwadago ta Najeriya ya ce ba zata sabu ba.

Nigeria Bukola Saraki (picture-alliance/AP Photo/S. Alamba)

Kakakin majalisa Bukola Saraki ya sa an yi wa kudirin karatun farko

Duk da yake an kai ga muhawara a kan wannan kuduri da ke jiran karatu na biyu a majalisar tarayyar Najeriyar, amma da alamun akwai ra'ayoyi mabambanta a tsakanin ‘yan majalisar da ma yadda suke kallon batun.

Ko da yake masu goyon bayan wannan kuduri na hangen kafar samun makudan kudaden da ake zargin an sace daga gwamnatin Najeriyar da suka wuce, amma akwai tsoron illar da wannan zai iya yi ga yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Batun matsalar yaki da cin hanci da rashawa na daya daga cikin kabulalen da ke fuskantar Najeriyar a yanzu, musamman koma bayan da ake fuskanta a fannin yaki da masu cin hanci da rashawa a kasar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin