Najeriya na shirin gudanar da noman zamani | Siyasa | DW | 25.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya na shirin gudanar da noman zamani

Mahukuntan Najeriya suka ce damunar bana na fuskantar barazana sakamakon karuwar cutuka, lamarin da ke zama koma baya a harkokin noma. Saboda haka ne gwamnonii suka kudirin aniyar taimaka wa manoma.

Har ya zuwa yanzun dai tarrayar Najeriyar na tsallen murnar samun rara ta akalla dala milliyan biyar a kullu yaumin sakamakon sabon shirin noman shinkafa da gwamnatin kasar ta kai ga runguma a halin yanzu. Sama da manoma miliyan 14 ne dai ke amfana a shirin da ke zaman sabuwa ta hanyar kyautata rayuwa ta 'yan kasar da samar da kudade na shiga ga manoma. To sai dai kuma gwamnatin tarrayar Najeriyar na kukan sabuwar barazanar da noman ke fuskanta a bana sakamakon bullar tsuntsaye dama  tsutsotsi da karuwa ta sumoga a iyakoki nata.

A wajen wani taron majalisa ta tattali na arzikin kasar dai, ministan noma na kasar Chief Audu Ogbe ya shaida wa gwamnonin bullar barazanar da ka iya babbar illa ga masu noman masara dama shinkafa. Barrister Mohammed Abdullahi Abubakar na zaman gwamnan jihar Bauchi kuma daya daga cikin gwamnonin da suka yi wa manema labarai  jawabi bayan kamalla taron.

 

A karon farko gawamnatoci na jihohi na shirin samar da akalla motocin noma sama da dari a ko'ina da nufin iya kaiwa ga kaddamar da shirin noma na zamani cikin watan da ke tafe a fadar gwamnan jihar Zamfara.  Ya zuwa ga daminar da ta shude dai Najeriyar ta yi nasarar noman shinkafar da ta kai ton miliyan uku a cikin biyar din da take da bukata a kokari na ci da kai dama sayarwa ga makwabta nata.

.

 

Sauti da bidiyo akan labarin