Najeriya na fafutukar yaƙi da cutar Ebola | Labarai | DW | 16.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya na fafutukar yaƙi da cutar Ebola

Gwamnatin jihar Lagos ta ce tana ba da horo ga masu aikin sa kai kimanin 800 domin yaƙi da cutar Ebola.

Gwamnatin jihar Lagos wacce ta ƙaddamar da shelar ta neman masu aikin sa kan tun makon jiya, na da zumar cike ratan da ake da shi na ma'aikatan jinya. Saboda yajin aikin likitocin da aka kwashe sama da makonnin shidda ana yi.

Wani kakakin gwamnan jihar Hakeem Bello, ya ce ma'aikatan za su riƙa bi saƙo-saƙo na birnin domin neman waɗanda suka yi cuɗanya da masu cutar ta Ebola domin faɗikar da su don samun kulawa.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar