Najeriya: Muhammadu Buhari ya rantsar da ministocinsa | Labarai | DW | 21.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Muhammadu Buhari ya rantsar da ministocinsa

Shugaba Buhari na Najeriya ya rantsar da wakilan majalisar ministocinsa inda ya nada Timipre Silva mukamin karamin ministan mai.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a wannan Laraba ya rantsar da membobin majalisar ministocinsa inda ya nada sabon mukamin karamin ministan albarkatun mai a majalisar mai ministoci 43.

Har yanzu dai Shugaba Buharin ne zai ci gaba da rike mukamin ministan mai kamar yadda yake tun a  wa'adin mulkinsa na farko, sai dai ya nada Timipre Silva a matsayin ministan kasa na albarkatun mai.

Shi dai Silva da ke zama tsohon gwamnan jihar Bayelsa, ya maye gurbin Emmanuel Kachikwu da ya kasance wakilin Najerya a kungiyar OPEC.

Zainab Ahmed za ta ci gaba da rike mukaminta na ministar kudi.