Najeriya: MDD ta janye wasu jami′an agaji | Siyasa | DW | 10.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: MDD ta janye wasu jami'an agaji

Sakamakon tsanantar hare-haren Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, Majalisar Dinkin Duniya ta janye wasu ma'aikatanta da ke aikin jinkai.

Ayyukan jin kai a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya ya fada cikin mawuyacin hali bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta janye ma’aikatan jin kai 260 a daidai lokacin da daruruwan ‘yan gudun hijira ke turuwa zuwa Maiduguri. Majalisar Dinkin Duniya dai ta tabbatar da cewa akwai sabbin 'yan gudun hijira fiye da 30,000 da suka isa Maiduguri daga yankunan Baga da ake gwabza fada tsakanin mayakan Boko Haram da sojojin Najeriya.

Kafin shiga wannan yanayi, dubban ‘yan gudun hijirar na fama da matsaloli na karancin abinci da sauran abubuwan rayuwa. Ana cikin haka ne kuma Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da janye wasu ma’aikatan jin kai guda 260 a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya saboda tsanantar hare-haren Boko Haram a ‘yan kwanakin nan.

Janyewar ma’aikatan zai haifar da wagegen gibi a kokarin da hukumomi ke yi na magance matsalolin ‘yan gudun hijirar wadanda aka kiyasta cewa sun haura miliyan biyu. Gwamnan jihar Borno Kashim Shetima ya ziyarci wuraren da aka tsugunar da sabbin ‘yan gudun hijirar inda ya bada tabbacin gwamnati na taimaka musu

Sauti da bidiyo akan labarin