1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mazauna a wasu yankuna na jihar Borno na tserewa

November 12, 2018

Yayin da Boko Haram ta yi barazanar kai karin hare-hare a kan kauyuka a Borno, mutane na tserewa saboda fargabar abin da ka iya faruwa.

https://p.dw.com/p/387Yw
Mutmaßlicher Boko-Haram-Angriff in Nigeria
Hoto: picture-alliance/AP/Jossy Ola

A daidai lokacin da rundunar sojojin Najeriya ta sauya shugabancin rundunar da ke yaki da Boko Haram wato "Operation Lafiya Dole" a karo na biyar cikin kasa da shekaru biyu, mazauna wasu kauyuka da ke bayan garin Maiduguri a jihar Borno na tserewa daga gidajensu zuwa wuraren da suke ganin ganin akwai cikakken tsaro saboda fargabar hare-hare daga mayakan Boko Haram.

Kusan kullum a 'yan kwanakin nan mayakan na Boko Haram na kai hari kauyuka da ba su da tazara daga Maiduguri, inda ko a daren ranar Asabar da tagaba ma hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa wato NEMA ta tabbatar da cewa mayakan Boko Haram sun kai hari kauyen Bale Shuwa, inda suka kashe wani mai fama da nakasa tare jikkata wasu da dama.

Mayakan sun kuma yi awon gaba da shanu da awaki da tumaki sama da 500 wanda suka kora su jeji ba tare da fuskantar wata turjiya daga jami'an tsaro ba.

Saboda haka ne mazauna kauyukan suka zabi tserewa daga garurwansu domin tsira daga hare-haren na mayakan na Boko Haram.

Malam Usman Abubakar wani mazaunin Jiddari Polo ne ya yi bayanin abin da ya sa shi tserewa zuwa Maiduguri.

"A kullum mutanen nan suna kai hari, abin ya tsorata mu, saboda haka muka ya dace mu gudu zuwa wurin da za mu samu sauki. Sojoji da sauran jami'an tsaro sun kasa ba mu kariya."

Zama cikin fargaba da rashin tabbas

A cewar al'ummomin kauyukan wanda yawancin ba su da nisan da ya wuce kilomita 5 zuwa 10 suna ganin lokacin da mayakan Boko Haram ke zuwa suna ajiye mata da aka daura musu bama-bamai da nufin kai harin kunar bakin wake a Maidugiri.

Nigeria Damasak Soldat Boko Haram Wandbild
Sojojin Najeriya sun ce suna bakin kokarinsu wajen tabbatar da tsaroHoto: Reuters/J. Penney

Sun ce mayakan na Boko Haram na musu gargadi na hallaka su tare da kona garuruwansu in har suka tona asirin ayyukansu da suke yi a wadannan yankuna.

Wannan ya jefa su zama cikin fargaba da tashin hankali musamman saboda yadda suka ji 'yan kungiyar na shirin kai hare-hare a birnin Maiduguri da ma wasu sauran sassan jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ficewar da mazauna wannan yankunan ke yi dai na zuwa a daidai lokacin da rundunar sojojin Najeriya ta sauya shugabancin rundunar da ke yaki da Boko Haram, abin da wasu ke alakantawa da tsanantar hare-haren mayakan na Boko Haram.

To sai dai jami'an tsaro sun ce suna bakin kokarinsu kuma yanzu haka ma sun karfafa matakai da suke dauka don magance fargabar da mutane ke fama da shi.

Alhaji Abdullahi Ibrahim shi ne kwamandan rundunar samar da tsaro ta farin kaya wato Civil Defense ya roki jama'a da su zauna a garuruwansu.

Masharhanta dai na ganin karfafa matakan tsaro a wadannan yankuna ya zama dole musamman don karfafa gwiwar jama'ar da suka koma garuruwansu don ci gaba da rayuwa.