Najeriya: Matasa za su iya tsayawa takara | BATUTUWA | DW | 31.05.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Matasa za su iya tsayawa takara

Bayan share tsawon lokaci ana fafutuka, a yau matasan Najeriyar sun yi nasarar samun damar taka rawa a cikin harkokin siyasar kasar bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kudirin dokar.

 

Akalla jihohin Najeriya 33 ne suka amince a bisa tsarin dokar da ta rage shekaru na takara cikin kasar da nufin samun dama ga matasa. Kafin daga baya shugaban kasar ya rattaba hannu a bisa dokar da ta kalli rage shekaru na takarar dan majalisar dokoki na jihohi daga 30 ya zuwa 25 a yayin da duk wani mai neman zama dan majalisar tarraya ya na bukatar kasancewa akalla shekaru 25.

Daga yanzu kuma duk mai son ya zama shugaban kasar zai kasance dan shekaru daga talatin da biyar amma sabuwar dokar ba ta sauya shekaru na gwamnoni da kuma 'yan majalisar dattawa ta kasar ba.

Nigeria - Jugenddemonstration not too young in Abuja (Uwais Abubakar Idris)

Daga cikin matasan da suka yi fafutuka don basu damar tsayawa takara

Tsalle na murna na zaman karatu na matasan da su kayi tururuwa domin ganewa idanunsa bikin na rattaba hannu kan dokar da suke yi wa kallon sabuwar kafa ta kai wa ya zuwa ga madafun iko bayan share tsawon lokaci suna zama 'yan kallo. Tun da farko Shugaba Buhari ya kira sabuwar dokar babbar dama ga matasa na kasar don nuna  kwarewarsu a cikin fagen siyasa.

Matasan Najeriya  sun shirya domin barin tasirinsu cikin harkoki na siyasa kamar yadda suka yi a sauran fage kamar kasuwanci da wasanni da sauransu. Babban kalubale ya zuwa yanzu dai na zaman iya hada kai a bangare na matasan da sune kaso sittin cikin dari na al'umma  kasar sannan kuma kaso hamsin da uku a cikin dari na masu kada kuri'a.

 

Sauti da bidiyo akan labarin