Najeriya: Mata masu koyo tukin jirgin sama | Zamantakewa | DW | 07.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Najeriya: Mata masu koyo tukin jirgin sama

'Yan mata da dama ne dai a Najeriya ke shiga aikin koyon tukin jirgin sama da ma sauran ayyuka da a da sai maza ake ganin suna yin irinsu, kamar aikin dan sanda.

A Najeriya ana samun matasa 'yan mata da ke ci gaba da nuna sha'awarsu a wurin koyon tukin jirgin sama da ma sauran ayyukan da suka shafi saka kayan sarki. Mata dai a kasar sun dade suna korafin yada maza suka mamaye irin wadannan ayyuka. Ayyukan da matan ke fuskantar kalubalen shiga a dama da su a cikinsu dai sun hadar da aikin dan sanda da soja da kuma tukin jiragen sama da makamantansu. 

Sauti da bidiyo akan labarin