Najeriya: Masu fashin jiragen ruwa sun sace mutane | Labarai | DW | 24.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Masu fashin jiragen ruwa sun sace mutane

Wasu masu fashin jiragen ruwa, sun sace ma'aikatan wani babban jirgin ruwa na kamfanin Peter Döhle na kasar Jamus, ciki har da Kaftan din jirgin a yankin kudancin Fatakwal.

Nigeria Piraterie (picture-alliance/dpa)

Masu fashin jiragen ruwa a Najeriya

Wasu mutane ne dai guda takwas dauke da makammai suka kai wa jirgin ruwan hari, wanda aka ce ya fito ne daga gabar ruwan Equatoriyal Guinea kuma ya gamu da 'yan fashin yayin da yake kokarin shiga tashar ruwan Onne da ke Kudu maso gabashin Najeriya. Sauran ma'aikatan jirgin guda 12 sun tsira, sannan kuma an mayar da  jirgin a yankin ruwan da ke da tsaro a cewar masu tsaron ruwan. Wani rahoto da hukumar kula da ruwaye ta kasa da kasa ta IMB ta fitar a makon da ya gabata,  ya ce an samu akalla hare-hare 121 a yankin ruwan Guinea da ke yammacin Afirka.