1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus: Dokar hana fita a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
March 30, 2020

A Najeriya al'umma na mayar da martani a kan jawabin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi, dangane da sababbin matakan dakile yaduwar annobar cutar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3aC1G
Nigeria Präsident Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari na NajeriyaHoto: Reuters/L. Gnago

Bayan dadewa ana masa kiraye-kiraye har ma da shagube, shugaban na Najeriya ya yi wa al'ummar kasar jawabi, inda ya tabo matakai sama da 14 da ya zayyana ana dauka domin dakile yaduwar cutar ta Coronavirus da ake wa lakabi da COVID-19. Jawabin da ya dauki hankalin 'yan Najeriya, ya sanya mayar da martani musamman kan hasashen tasirin da matakan zasu iya yi kai tsaye ga rayuwar mazauna jihohin Lagos da Ogun da kuma babban birnin tarayyar kasar Abuja. Daga karfe 11 na daren wannan Litinin din, za a dakatar da zirga-zirga har tsawon makonni biyu a johohin na Lagos da Ogun da kuma Abuja fadar gwamnatin kasar.

Akwai lauje cikin nadi a jawabin

BG Wasserverbrauch Anbauprodukte Afrika | Tomaten in Nigeria
Da yawan 'yan Najeriya sai sun fita kasuwa suke samun abin da za su ciHoto: Getty Images/AFP/Y. Foly

Sai dai masana na ganin akwai batutuwan da jawabin shugaban kasar bai tabo ba. Duk da muhimmancin matakan wajen katse hanzarin yaduwar cutar ta Coronavirus, ga Mallam Auwal Musa Rafsanjani na kungiyar CISLAC, na da ra'ayin cewa dungu shugaban ya yi a kan tallafin da za a bai wa marasa karfi a lokacin zaman gidan na makonnin biyu.

Ya tallafi zai isa ga talaka?

Ga mafi yawan 'yan Najeriyar dai, abin da yafi daukan hankalinsu shi ne yadda tallafin da aka ambata zai kai garesu, a lokacin hana zirga-zirgar. Ana dai cike da fatan wadannan matakai za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar ta Coronavirus a Najeriyar, da a yanzu yawan wadanda suka kamu ya zarta mutane 100.