Najeriya: Martani kan harin sansanin ′yan gudun hijira | BATUTUWA | DW | 18.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Martani kan harin sansanin 'yan gudun hijira

A Najeriya kungiyoyin kare hakin jama'a sun maida martani da lafazi mai zafi a game da harin da jirgin saman sojojin kasar ya kai akan sansanin ‘yan gudun hijira.

Harin da ya yi dalilin mutuwar mutanen da dama da jikkata wasu, inda Human Rights Watch ta ce lallai sai gwamnati ta biya diyya ga ‘yan uwan mutrtanen da suka mutu.

To hankula dai sun tashi kuma zukata sun baci biyo bayan wannan hari da ake ci gaba da alhini a kan yadda aka yi ya faru, duk da cewar mahukuntan sojan sun ce kuskure ne ya haifar da shi, abinda ya sanya kungiyar kare hakkin jama'a ta Human Rights Watch da ta kasance kan gaba a jerin kungiyoyin kare hakin jama'a da suka nuna bacin ransu a kan lamarin cewa dole ne gwamnatin kasar ta  hanzarta kula da lafiyar mutanen da suka jikkata a wannan hatsari da ma biyansu diyya, domin da ace ba kuskure ba ne to da lamarin ya zama laifukan yaki.

Lalube na dalilin afkuwar lamarin da ke  ake ci gaba da yi a dai dai lokacin da gwamnatin ta tura tawaga zuwa Maidugurin a kan wannan lamari, tambayoyi mabanbanta sun cika zukatan ‘yan Najeriya musamman ma dai ‘yan uwan mutanen da suka mutu, shin Najeriyar na da wani tsari na kare  fararen hula daga hare-hare a yakin da ta kwashe kusan shekaru bakwai tana yi da kungiyar  Boko Haram?

A yayin da ake da ci gaba da nuna damuwa na rashin sanin zahirin adadin mutanen da suka mutu da wasu ke ambato alkaluman da suka zarta na hukuma, ga Mrs Kayuata Giwa ta kungiyar mata masu muradin kare hakkokin jama'a da muhalli na bayyana cewa bisa abinda ya faru dole ne a sake lalle.

Ana dai nuna tsoron illar da wannan ka iya yi ga yaki da ta'adanci a Najeriya musamman 'yan gudun hijirara da suke kallon sansanoninsu a matsayin tudun mun tsira.

Sauti da bidiyo akan labarin