Najeriya: Mabambantan ra′ayoyi kan dokar hana bara a Kano | Siyasa | DW | 26.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Mabambantan ra'ayoyi kan dokar hana bara a Kano

Alarammomi da sauran al'umma na yin martani mabambanta dangane da matakin haramta gararambar kananan yara da sunan bara a birnin Kano.

Gwamnatin jihar Kano ta ce ba gudu ba ja da baya dangane da dokar hana bara a birnin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce ba gudu ba ja da baya dangane da dokar hana bara a birnin Kano

A ranar Talatar ce gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya nanata furucin cewar duk yaron da aka kama yana bara a birnin Kano to za a kama shi kuma akwai yiwuwar daukar matakin shari'a a kan malaminsa da kuma iyayensa lamarin da ke ci gaba da jawo kace-nace a birnin Kano.

Miliyoyin yara ne ke gararamba a fadin arewacin Najeriya da sunan yin bara. Wani abin takaici ma shi ne yadda ake ganin kananan yara da ba su wuce shekara biyar zuwa 10 ba, amma iyayensu sun sake su domin zuwa karatun allo nesa da gidajensu, wanda karshe za a ga sun bige da yin gararamba a gari da sunan bara. Wannan matsala dai ga alama ta fara ci wa mutane da hukumomi tuwo a kwarya har takai gwamnan Kano ya yi furucn daukar matakin kama yaran da kuma gurfanar da iyayensu a kotu, matakin da Alaramma Abdullahi mai Tsangaya ke cewar ya ba su mamaki.

A yawancin garuruwan arewacin Najeriya kamar nan a Dutse da ke jihar Jigawa, ana samun kanana yara da ke yawon bara

A yawancin garuruwan arewacin Najeriya kamar nan a Dutse da ke jihar Jigawa, ana samun kanana yara da ke yawon bara

Yawaitar yara da ke gararamba a birnin Kano da kuma karuwar barazanar tsaro da ayyukan tarzoma ya sa mutane da dama sun fara shiga cikin damuwa da matsalar karuwar almajiran, wannan ne ma yasa da yawa mutane ke lale marhabin da wannan mataki. Abubakar Ibrahim da ke cikin rukunin masu cewar matakin yayi dadi, ya ce idan aka zura ido nan gaba kadan za a yi faduwar guzuma 'ya kwance uwa kwance.

To amma wani magidanci da ya ce shi tsohon mabaraci ne ya soki lamirin wannan mataki yana mai cewar ya saba da ka'ida.

Wasu almajirai a birnin Kano sun ce ba su da masaniyar wannan doka amma tun da an yi haka za su tattara ne su koma gida.

Da yawa daga cikin yaran na zargin malamansu ne ke tura su zuwa bara don kawo musu kudi

Da yawa daga cikin yaran na zargin malamansu ne ke tura su zuwa bara don kawo musu kudi

Miliyoyin kananan yara ne ke gararamba da sunan bara a biranen arewacin Najeriya, kuma galiban sukan yi rayuwa ne cikin kaskanci da muzgunawa daga kodai malamai ko garada a makaranta ko kuma daga wasu bata gari. Babban misali a kwana kwana nan shi ne wani almajiri mai shekara tara da aka tura wata tsangaya da ke Sumaila da ke jihar Kano daga jihar Jigawa, kuma a makarantar yaron ya ce malaminsu ya sa musu harajin Naira 40 kullum. Rashin kawo wannan kudi ne yasa malaminsu mai suna Malam Nafiu Gomo ya daure masa hannuwa ya kulle shi tsawon kwanaki biyu da wuni guda har ta kai yanzu hannun yaron ya rube ya nakatsa.

Tuni kwamishinan shari'a na jihar Jigawan Barister Musa Adamu Aliyu ya rubuta wasika ga takwaransa na Kano domin a dauki matakin gurfanar da wannan alaramma a gaban kuliya.

Da yawa daga cikin mutane na ganin cewar wannan doka za ta rage matsalar muzgunawa da kananan yara ke fuskanta da sunan bara.

Sauti da bidiyo akan labarin