1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kotu ta bai wa Elzakzaky damar ganin likita

February 24, 2020

Rashin bai wa Elzazzaky da matarsa damar ganin likitocin da za su rika duba lafiyarsu a kurkukun jihar Kaduna inda ake tsare da su, ya sanya kotun ta Kaduna sake dage zaman sauraran kararsu.

https://p.dw.com/p/3YLYY
Hotunan sheikh Ibrahim el-zakzaky a hannun magoya bayansa
Hotunan sheikh Ibrahim el-zakzaky a hannun magoya bayansaHoto: AFP/S. Adelakun

Yanzu dai tabbas an dage karar da malamin da matarsa Zeenat da gwamnatin Kaduna ta shigar har sai ranar 23 ga Watan Afrilu mai zuwa. Kotun kuma ta umarci gidan yarin na Kaduna da su rika bai wa likitocin Elzazzaky damar zuwa duba lafiyar jikisa. Tun da karfe 9 na safiya, aka kawo Sheikh din cikin tsattsaurar matakai na tsaro tare da matarsa Zeentat cikin wani babban koton Kaduna kewaye da jami’an tsaro, domin karanta musu laifukan da ake tuhumar su akai. Sojoji da ‘yan sanda da sauran kungiyoyin tsaro na ‘yan sa kai ke ta sintiri a manyan titunan Kaduna domin zama a cikin shirin ko ta kwana, yayin da babbar kasuwar jihar Kaduna ta kasance a kulle ruf. 
A yau ma dai, kotun ta sake dage zaman yau ne, saboda rashin isasshen lafiyar da ke a jikin malamin da matarsa, al'amarin da ya sanya alkalin kotun sake dage zaman, tare kuma ba bayar da umarnin tabbatar da ganin cewa likitocin suna zuwa duba lafiyarsu,domin ba su damar zuwa kotun dan sauraran dukkanin kararrakin da ake tuhumar su akai. 
Barista Sadau Garba Lawan da ke kare Sheihk Zazzaky ya kuma kara da cewa babbar matsalar da aka samu a wannan lokacin ita ce na rashin hadin kai da ake samu tsakanin jami’an tsaro da ke gadin gidan kurkukun na Kaduna, wadanda ke hana likitocin Elzazzaki ganinsa, don duba lafiyar jikinsa kamin gabatar da shi a gaban kuliya. 
Sadau ya nunar da cewa muddin dai ana san yin adalci da kuma tabbatar da gaskiyar da ake bukata, to ya zama wajibi kotu ta bayar da umarnin Sheihk Zazzaky, ya rika ganin likitocinsa dan samun damar duba lafiyar jikinsu shi da matar yadda ya kamata. 
Idan dai ba a manta ba, tun bayan dawowar Sheihk Zazzaky daga kasar India wajen neman lafiyar jikinsa a kasar waje, wannan shi ne karan farko, da aka ganshi da matarsa cikin kotun Kaduna saboda rashin isasshen lafiyar jiki. 
Barista Bayero Dari, shi ne dai lauyan da ke kare bangaren gwamnatin jihar Kaduna a kotun, ya kuma gamsu da matakin da kotun ta dauka na bai wa likitocin da ke duba lafiyar Elzazzaky damar ganinsa. Ya ce mun amince da matakin da koton ta dauka na ganin an kyale likitocinsa suna zuwa duba lafiyar jikinsa. Dari ya ce, yana da kyau a bar shi,ya sami lafiyar jikinsa domin amsa tambayoyin da ake zarginsa akai.
A ranar juma'ar nan da ta gabata ce, wata kotun da ke sauraran karar almajiran Elzazzaky da aka kama tun shekara ta 2015 bayan barkewar rikici tsakanin sojoji da ‘yan Shi'ah a garin Zaria, ta sako sauran almajiran da ke tsare a babban gidan yarin Kaduna kamar dai yadda Barista Haruna Magashi da ke kare almajiran ke cewa:
''Ya ce wadanda kotun Kaduna ta sako sun kai mutane 90, kuma muna ganin cewa yanzu haka babu wani da aka tsare da shi a sakamakon wannan matsalar.''
Haruna ya kara da cewa abubuwan da ake tuhumarsu akai, ba su aka same su da shi ba, a cewarsa hakan ne ya sanya kotun gaggauta sakinsu, domin komawa jihohin da suka fito. Su kuwa dai kungiyoyin kare hakkin bil Adama da masu gwagwarmayar zaman lafiya sun bukaci ganin adalci a karshen wannan shara’ar.

Nigeria Abuja Proteste von Schiiten des Islamic Movement
Hoto: picture-alliance/AA/A. A. Bashal
Mata mabiya Shi'a da goyon bayan El-Zakzaky a jihar Kaduna
Mata mabiya Shi'a da goyon bayan El-Zakzaky a jihar KadunaHoto: picture alliance/AP Photo/Sunday Alamba