Najeriya: Kotu ta kwace kadarorin Diezani | Labarai | DW | 08.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Kotu ta kwace kadarorin Diezani

Wata Kotu a jihar Legas ta kwace kadarori da rukunin gidaje da darajarsu ta kai Dala miliyan 37 mallakin tsohuwar ministar man kasar Diezani Alison-Madueke.

Wata Kotu a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta kwace kadarori da wani rukunin gidaje da darajarsu ta kai Dalar Amurka miliyan 37,mallakin tsohuwar ministar albarkatun man kasar Diezani Alison-Madueke. Mai shari'a Chuka Obiozor ya kuma umarci tsohuwar ministar da ta gaggauta maido da kudadden hayar da aka biya ta daga wadannan gidajen.

Wannan ba shi ne karon farko da ake kwace kadarorin tsohuwar ministar bisa zarginta da sace tare da yin facaka da kudin kasar ba, zargin da ta sha musantawa.