Najeriya: Korafi kan kin sake zaben jihohin Rivers da Bauchi | BATUTUWA | DW | 18.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Korafi kan kin sake zaben jihohin Rivers da Bauchi

Jam'iyyar APC mai mulki ta yi watsi da sabon matakin da hukumar INEC ta dauka a game da zaben gwamna na jihohin Bauchi da Rivers, bayan da hukumar ta janye daga maimaita zabe zuwa ga ci gaba da tattara sakamako.

Jam'iyyar APC ta bayyana matakin da tamkar amai ne da INEC ta lashe a yayin da ta zargi Shugaban kasar da laifin cewa uffan kan lamarin,  amma hukumar zabe dai na mai cewa tun da an riga an yi zabe kuma an sanar da sakamakon har an mika shi ga wakilan jam'iyyu, hargitsa aikin tattara shi da wasu zauna gari banza da ma jami'an tsari a jihar Rivers suka yi ba zai sa a sake wani sabon zabe ba. Tuni 'ya 'yan jam'iyyar PDP ta ‘yan adawa suka fara murna a kan matakin hukumar zaben da a fili suke ganin sun kama hanyar samun nasara, domin kuru'un da hukumar zaben ta sake hallatasu bayan soke su da farko sun sauya yadda suke kalon zaben.

Kartoon Nigeria APC Crisis

Buhari na shan suka daga jam'iyyun APC da PDP kan batun sake zaben gwamnonin.

A yayin da hukumar zaben Najeriya ta bayyana takaici na zargin rawar da sojoji suka taka a zaben jihar Rivers, tuni shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi alkawarin ba zai sauya sakamakon da za'a samu a jihohin da za'a maimaita zabubukan ba. Shugabanin al'umma na ci gaba da jan hankalin ‘yan siyasa da su kasance masu bin doka a kan sakamakon zabe ta hanyar amincewa da samun nasara ko akasin hakan.

Sauti da bidiyo akan labarin