Najeriya: Kokarin murkushe ′yan jarida | Siyasa | DW | 02.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Kokarin murkushe 'yan jarida

A Najeriya kungiyoyin farar hula da ke fafutukar kare hakkin dan Adam da 'yan jaridu sun bayyana damuwa a kan ci gaba da farma 'yan jaridu a kasar a wani abu mai kama da raguwar ikon fadar albarkacin baki da suke da shi.

Afrika Pressefreiheit l Zeitungen in Nigeria

Kalubale ga 'yancin 'yan jarida a Najeriya

Karuwar wannan matsala ta farma 'yan jaridu ta hanyar kama su da kuma kulle su saboda kawai sun fadi gaskiya a Najeriyar, a wani mataki da ake wa kallon tamkar kokarin rufe bakinsu, ya kasance mai tayar da hankali ga 'yan jaridun kansu da ma kungiyoyin fara hula.  'Yan jaridun da wakilan kungiyoyin sun tattauna a kan wannan batu da nufin nemo mafita, musamman yadda kungiyar kare hakin dan Adam ta kasa da kasa Amnesty International ta gano afkuwar irin wannan har sau 60 a shekara ta 2019 da muke ciki. Daya daga cikin matakan da aka dauka shi ne na samar da wata kafa ta Internet da cibiyar nazarin aikin jarida ta Premium Times ta samar, domin 'yan jaridun su rinka shigar da kokensu bisa cin zarafi ko kama su da aka yi a matsayin hanyar samun mafita.

Symbolbild Presse

Najeriya: 'Yan jarida na fuskantar kalubale

Martanin kungiyoyi masu zaman kansu

Mr Seun Bakare na kungiyar kare hakin dan Adam ta Amnesty International ya bayyana hadarin da ake fuskanta yana mai cewa'yancin fadar albakacin baki na fuskantar barzana kuma in ba a hada kai an tunkari matsalar ba, to babu wanda zai taimaka, abin da zai iya rusa 'yan jaridar cikin gaggawa. A nada bangaren, Abiodun Baiyewa ta cibiyar Global Rights ta ce nauyi ne a kan kowa ya tashi don tunkarar wannan matsala. Batun kudurin doka a kan kafofin sada zumunta da majalisar dokoki ke aiki a kanta dai, na cikin abin da aka tattauna. Babu shakka aikin jarida na fuskantar sabon kalubale a Najeriyar, sakamakon karuwar matsawa 'yan jaridar a kokari na rufe musu baki, abin da aka yi amannar ba gudu ba ja da baya.

 

Sauti da bidiyo akan labarin