Najeriya: Kokarin magance hasturan ababen hawa. | Himma dai Matasa | DW | 03.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Najeriya: Kokarin magance hasturan ababen hawa.

A sakamakon yawan samun hadarurruka da ke faruwa a titunan Najeriya wani matashi mai suna Prince Fedelis Nnadi da ke a Abuja ya bullo da wata Kungiya mai suna(AFRI) wato Accident prevention& Rescue Initiative

Ita dai wannan kungiyar da ke fafutukar ganin ta tallafa wa wadanda suka fuskanci hatsarin kan hanya wato AFRI a takaice, ta bayyana ne sakamakon wani bawan Allah mai suna Prince Fedelis Nnadi, wanda shi da kansa ya hadu da mummunan hatsari shi da iyalan sa a shekaru sama da bakwai da suka gabata, a inda ya sha matikar wahala shi da iyalan sa gami da asarar dimbin dukiya koda yake babu asarar rayuka. Ganin matsanancin halin da ya fada gami da kasancewar yawan mace-macen da ke afkuwa a Najeriya, hadarin kan hanya na kasancewa na biyu wajen hallaka bil adama a Najeriya. Price Fedelis Nnadi ya karawa tashar DW bayanin yadda AFRI ta samo asali. 

‘’Wanda ya kirkiri wannan kungiyar wato ni,  wanda kuma na taba  fuskantar hatsaari, na yanke shawarar cewar lallai akwai bukatar mu yi wani abu. Sabi da a irin abunda na fuskanta a lokacin da hatsarin ya same ni, babu wani jami’i ko wani kwararre da ya kawo min dauki, in banda mutanen kan hanya. Gaskiya nayi asarar dukiya mai yawa kuma na wahala koda yake dai  ba wanda ya rasa ransa. Wannan shi ne dalilin da ya sanya fara wannan fafutukar domin kara inganta rayuwar wadanda suka tsinci kan su a hadarurruka.’’

Kungiyar ta AFRI wacce ta fara daga mutum daya, yanzu haka tana da sama da mutane 500 a matsayin masu kundin bala wajen tallafawa wadanda suka fuskanci hatsarin kan hanya a Najeriya Prince Fidelis Nnadi yac

e.

 "Nasarorin da muka samu zan iya cewar a shekara ta 2006, lokacin da muka fara wannan tafiyar mun shiga ka'in da na’ain wajen fadakar da alumma, akan masifar da ke tattare da wannan annobar ta hatsarin ababen hawa. Mun kuma tallafa wa wadanda suka sami hatsari masu yawa, muna kuma kewayawa jihohi a Najeriya don fargar da jama’a, baya ga tattara bayanai daga ‘yan sanda da mafi yawanci sune suke fara samun bayanai hatsarin kan hanya"

Ga Nkwankwo Peace wacce ta kasance a fafutukar ceto wadanda suka tsinci kansu a hadarin kan hanya cewa take:

‘’Aikace- aikacen AFRI a bayyane ne yake ga jama’a, a dangane da gudummar da take bayar wa. A wasu lokuta mukan bi Prince Fedelis kafafen watsa labarai a inda muke gudanar da shirye shirye akan yin hattara yayin tafiya a ababen hawa domin kuwa yaruwar mutane tana mahimmaci  don haka ayi tuki a hankali da lura’’

Ita ma dai Ezuaworie Blesssing nuni ta yi da cewar:

‘’Mr Prince wanda ya fuskanci hatsari kan hanya ya kasance mai matukar son ganin ya ceci wadanda suka tsinci kan su a hadari. Zan so na baiwa gwamnati shawara akan duba hanyoyin da za su tallafa wa wannan kungiyar ta yadda za a iya kawo raguwar samun hatsarurrukan kan hanya a Najeriya.’’

Babban dai burin AFRI shi ne samun gagarumin sauyi wajen yadda masu amfani da ababen hawa suke tuki a kan hanya gami da kara samun masu bada kundin wajen ayyukan ceto, ga wadanda suka samu kan su cikin hatsari kan hanya.

Sauti da bidiyo akan labarin