Najeriya: Kokarin dinke baraka a tsakanin 'yan kasar
February 28, 2019Talla
Tuni dai shugaban kasar ya fara batun hada kai dama kafa gwamnatin da ke da wakilcin kowa, bayan wani yakin neman zabe mai zafin da kasar ta dauki lokaci tana fuskanta. An dai kai ga karawa tsakanin 'yan boko da talakawa na kasar da tsakanin al’ummar kudancin kasar da arewa dama tsakanin mabiya manyan addinan kasar guda biyu. To sai dai kuma an kare da gudanar da zaben da ke dada nuna alamun baraka cikin kasar, bayan wata musayar yawu mai zafi a cikin kafafe na zumunta a tsakanin matasan na Kudu da na arewa game da yadda sakamakon ya kasance.