Najeriya: Kisan mutane a jihar Kaduna | Labarai | DW | 07.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Kisan mutane a jihar Kaduna

Akalla mutane 21 suka hallaka sakamakon wani harin 'yan bindiga a karamar hukumar Zangon Katab da ke kudancin Kaduna a arewacin Najeriya.

Wani mai suna Luka Biniyat, kakakin hadin gwiwar kungiyoyyin fararen hula a yankin, ya shedawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP da cewar adadin mamatan ka iya zarta wadanda hukumar 'yan sandan jihar ta bayar daga 21 zuwa 33. Ko baya ga mamatan dai rahotanni daga yankin sun ce an samu akalla mutun uku da suka ji rauni a yayin harin, kana kuma tuni aka kafa dokar tabaci a yankin.

Duk da yake ba wata kungiyar da tafito fili ta dauki alhakin klai harin, shaidun gani da ido sun tabbatar da manema labarai da cewar wasu mutane ne kan babura dauke da muggan makamai suka kaddamar da hare-haren a kauyuyukan biyar galibinsu mabiya addinin Kirista a karamar hukumar Zangon Katab.