1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Fargaban al'umma a kan sha'anin tsaro

Abdullahi Maidawa Kurgwi AH
May 11, 2018

A Najeriya shugabanin kungiyar Miyetti Allah a yankin jihohin Arewa maso Tsakiya, sun bukaci ganin hukumomin tsaro na daukan matakai na zahiri don tabbatar da tsaro.

https://p.dw.com/p/2xY6N
Nigeria Ölrebellen
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

To wannan kiraye kiraye da shugabannin kungiyar ta Miyetti Allah suka yi dai ya biyo bayan irin kamen da jami'an tsaron suka yi ne a tsakanin makon jiya da kuma wannan mako. Inda ko da a ranar Talata da ta gabata ma dai rundunar sojin Najeriya ta gabatar wa manema labarai wasu 'yan bindiga da ta ce ta kamo su da manyan makamai a kauyen Tsedum da ke cikin karamar hukumar Guma  ta Jihar Benue. Ita ma rundunar 'yan sanda ta gabatar wa manema labarai wasu da take zargi da kai hare-hare kan al'ummomi da ke tsakanin Jihohin Benue Nasarawa da Taraba, cikin su akwai wani da ake kira Morris Ashwe, dan hasalin yankin Mbajimba da ke karamar hukumar Katsina Alla cikin jihar Benue. wanda ya amsa cewar shi ne ke samar da makamai ga fittacen dan bindigar nan Tarwase Akwaza da jami'an tsaro ke nema ruwa a jallo.