Najeriya: Kalaman batanci na tada kura a siyasa | Siyasa | DW | 16.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Kalaman batanci na tada kura a siyasa

Wannan na zuwa ne bayan da hukumar zaben ta Najeriya ta mika takardun shaidar rijista ga karin jam'iyyu biyar a Abuja.

Kokari na toshe duk wata kafa da ka iya amfani da ita a tsakanin jam'iyyun siyasar Najeriyar domin tada fitina ta hanyar furta kalamai na nuna kyama da batanci ya dauki hankalin hukumar zaben mai zaman kanta ta Najeriya, da ta bayyana bukatar nuna hali na siyasa bada gaba ba a kasar, a daidai lokacin da take ci gaba da shirye-shiryen zabubbukan da ke gabanta.

Shugaban hukumar zaben ta Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ce abu ne mai muhimmanci ga ‘yan siyasa su fahimci hakan, musamman a daidai lokacin da aka samu karin jam'iyyu a Najeriyar da a yanzu suka kai 45 baya ga wasu kungiyoyi siyasa har 95 da yanzu haka suke neman a yi masu rijistar zama jam'iyyun siyasa.

Shugabanin sabbin jam'iyyun siyasar da aka mikawa takardun rijstarsu a ganawar da shugaban hukumar zaben ya yi da shugabaninsu suna masu nuna bukatar samun hadin kai da dorewar dimokradiyya a matsayin hanyar da jama'a ke da dama ta zaben wakilansu Injiniya Yagbagi Yusuf Sani shugaban jamiyyar Action Democratic Party daya daga cikin sabbin jamiyyun biyar a Najeriyar.

A karon farko dai an samu jamiyya ta matasa a Najeriyar kamar yadda shugabanta Yakubu Shandam shugaban jam'iyyar Youth Progressive Party ya bayyana.

To sai dai a yayinda hukumar zaben Najeriyar ke wannan aiki akwai korafe-korafe a game da ci gaba da aikin rijistar masu zabe da aka shiga mako na takwas ana yi, Abin jira a gani shi ne kamun ludayar sabbin jamiyyun siyasar da ma sauran wadanda suka dade ana gogawa da su, domin a bayyane take cewa daga cikinsu ne wadannan suka fito don gwagwarmaya a zabubbukan da ke tafe a tarayyar ta Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin