Najeriya: ISWAP ta kai wa sojoji hari | Labarai | DW | 06.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: ISWAP ta kai wa sojoji hari

An yi ba ta kashi tsakanin sojojin Najeriya da mayakan Boko Haram bangaren ISWAP a kauyen Jakana mai nisan kilomita 45 da Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa sun ga gawarwakin sojojin Najeriya da kuma mayakan ISWAP yayin da su ke wucewa a titin Maiduguri zuwa Damaturu, kafin daga bisani sojojin su rufe hanyar. Koda a ranar Asabar din da ta gabata ma, an gwabza irin wanann fada bayan da mayakan na ISWAP su ka kai hari sansanin sojojin Najeriya a Jakana, inda sojoji hudu suka mutu wasu 11 kuma suka jikkata, yayin da mutane shida kuma suka sheka barzahu a bangaren mayakan na ISWAP. Wannan hanya dai a yanzu ta zama abin tsoro, sakamakon yadda ake yawan gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan Boko Haram. Yanzu haka rufe hanyar ya rutsa da dubban mutane da ke son fita ko kuma shiga Maiduguri.