1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kotu ta sauke shugaban NFF

Abdul-raheem Hassan
July 2, 2018

Gwamnatin Najeriya ta umarci hukumar kwallon kafa ta kasar ta bi umarnin hukuncin kotu da ya rusa shugabancin hukumar karkashin jagorancin Amaju Pinnick.

https://p.dw.com/p/30hTl
WM Südafrika 2010 Griechenland vs Nigeria Flash-Galerie
Hoto: AP

Hukuncin kotun kolin ya amince da Chris Giwa a mastayin halastaccen shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya wato NFF, sabon shugaban NFF din ya halarci ofishin hukumar kwallon kafar kasar tare da rakiyar jami'an 'yan sanda a wani mataki na cika umarnin kotun da ta mayar da shi kan mukaminsa.

Tun a shekarar 2014 ake ta kwan gaba kwan baya kan shugabancin hukumar kwallon kafar ta Najeriya, inda Chris Giwa ya yi ikirarin lashe zaben shugabancin hukumar, sai dai hukumar FIFA ta yi watsi da sakamakon zaben tare da bukatar sake sabon zabe bisa zargin gwamnati da yin katsalandan.

A baya dai FIFA ta dakatar da Najeriya bisa zargin gwamnati da yin shishigi a harkokin gudanar da zaben hukumar kwallon kafar kasar. A yanzu dai akwai fargabar hukuncin kotun wadda ta soke shugabancin hukumar ka iya bude sabon babin takun saka tsakanin Najeriya da hukumar kwallo kafa ta duniya FIFA.