Najeriya: Hawan daushe a jihar Kano | BATUTUWA | DW | 12.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Hawan daushe a jihar Kano

Duk da fargabar barkewar rikici da jama'a ke ciki, an gudanar da hawan Daushe da bisa al'ada Sarkin Kano ke jagoranta ba tare da wata matsala ba.

 

A wannan Litinin ake yin hawan,wanda bisa al'ada Sarkin Kano ke yin hawa daga gidansa zuwa gidn mahaifiyarsa domin yi mata gaisuwar sallah, da fari dai an shiga fargabar samun matsala a hawan daushen na bana la'akari da zaman doya da manja kan kwan gaba kwan baya tsakanin gwamnatin Kano da fadar masarautar jihar,  sai dai samun bakuncin Shugaban kasar Guinea, Alpha Conde yasa an sami hadin kai da kuma zama inuwa guda tsakanin gwamnan da Sarkin,  lamarin da mutane ke murnar cewar an fara samun dinkewar barakar da ta kunno kai a tsakanin mutanen biyu.

Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano

An kwashi watanni ana takun saka a tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sunusi na biyu

A ranar hawan sallah, an sami daidaito, har ma an yi musabaha tsakanin gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sunusi na biyu, sai dai kuma daga bisani an yi ta samun karafkiya, inda fadar masarauta ta yi umarni ga dukkan hakimai da su shigo birnnin Kano domin hawan daushe da ake yi a wannan Litinin, amma kuma sanarwar umarnin  kauracewa hakan da gwamnatin Kano ta bayar ya nuna karara cewar akwai sauran rina a kaba, wato ana cigaba da zaman cin kunamar kadangare tsakanin gwamna Ganduje da Sarkin Kano.

 

Emir von Kano Alhaji Dr Ado Bayer Thron 50 Jahrestag

An yi Hawan Daushe cikin yanayi na tsaro

A  yayin da mutane suka zura ido dan ganin yadda za ta kaya a ranar hawan daushen; sai kuma aka sami sanarwar cewa kowanne hakimi ya shigo birni domin halartar hawan daushe kasancewar zuwan babban bako, wato Shugaban kasar Guinea Alpha Conde wanda ya shigo jihar domin halartar wannan hawa. Yanzu haka,  galiban ma'abota harkokin masarauta na ta bayyana farin ciki dangane da yadda aka sami halartar hakimai zuwa wannan hawan dushen.

 

A ranar Lahadin da ta gabata aka tsananta matakan tsaro a birnin Kano, haka kuma hakimai da sauran mahaya dawaki sun yi kwalliya da kayyyaki na al'ada yayin gabatar da wannan hawa wanda manyan baki daga ciki da wajen Najeriya suka halarta, haka kuma mai girma gwamna Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da tawagarsa sun yi rakiya ga Shugaban kasar Guinea wanda ya zamo babban bakon hawan daushen bana, shi kuwa Sarkin Kano ya karbi gaisuwa a cikin yanayin kwalliya yana haye akan rakumi.

Sauti da bidiyo akan labarin