Najeriya: Gwamnati za ta nemi diyya ga Afirka ta Kudu | Duka rahotanni | DW | 03.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duka rahotanni

Najeriya: Gwamnati za ta nemi diyya ga Afirka ta Kudu

A Najeriya a daidai lokacin da 'yan kasar ke nuna bacin ransu kan kisan 'yan Najeriya da lalata masu dukiyoyi a rikicin kyamar baki a Afirka ta Kudu, gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin neman diyya ga Afirka ta Kudu.

Ya zuwa yanzu dai bakuna na 'yan kasar na kumfa. Haka kuma rayukan mahukunta sun baci sakamakon kisa na kyamar bakin da ke ta karuwa a kasar Afirka ta Kudu a halin yanzu. Akalla 'yan Najeriya uku ne dai aka kai ga hallakawa a sabon jeri na zanga-zangar da ko bayan nan ta kalli kona cibiyoyi na kasuwanci na 'yan kasar a garing Gauteng da ke kasar ta Afirka ta Kudu. Wata sanarwar fadar gwamnatin Najeriyar dai ta ce Shugaba Buhari yana shirin tura manzo na musamman da nufin bin diddigin abun da ke faruwa a kasar sannan kuma Tarrayar Najeriyar na neman diyyar ta'addin da 'yan kasar suka fuskanta yayin rigingimu.


Unruhen in Südafrika (AFP/G. Sartorio)

Wasoso a shagunan baki a Afirka ta Kudu

Zuwa dakan da ya dara sako dai ana kallon matakin Tarrayar Najeriya a matsayin kama hanyar kaiwa zuwa wani rikicin diplomasiyya a tsakanin manyan kasashen na Afirka Biyu. A cikin watan Oktoban da ke tafe ne dai aka tsara wata ganawa a tsakanin shugabanni na kasashen guda biyu da nufin nazarin jerin matsalolin da ke zaman barazana mai girma ga makomar ciniki da zumuncin da ke tsakani mai tasiri. 

Rahotannin da ke fitowa daga birnin Ikko dai sun ce  masu zanga-zanga sun kai hari a kan babban kantin Shopreite na kasar ta Afirka ta Kudu a unguwar Lekki sannan kuma da offishin kamfanin sadarwar MTN da ke a Apapa. To sai dai kuma sabbabi na matakan da suka kalli wani sammaci ga jakadan Afirka ta Kudun a Abuja, ba su shirin rikidewa zuwa ramuwa irin ta gayya mai zafi a a fadar Geoffry Onyeama da ke zaman ministan harkokin wajen Tarrayar Najeriyar.

Südafrika fremdenfeindliche Angriffe auf Migranten (AFP/R. Jantilal)

Wani dan Malawi da ya fuskanci farmaki irin na kyamar baki a Afirka ta Kudu

Kasashen guda Biyu dai na zaman na kan gaba ga batun ciniki a daukaci na nahiyar ta Afirka kuma a fadar Farfesa Usman Mohammad dake shugabantar tsangayar siyasa ta kasa da kasa, Afirka ta Kudu na da bukatar gamsar da kusan kowa game da irin shirin da take da shi na kai karshen matsalar.
Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa a tsakanin hukumomin kasashen guda biyu da matasan na Afirka ta kudu da ke ta korafin kwace musu aiki daga baki.

Sauti da bidiyo akan labarin