Najeriya: Alkalin alkalai zai gurfa a gaban kotu
January 12, 2019Kakakin kotun da'ar ma'aikatan Najeriya Ibraheem Al-Hassan wanda ya sanar da wannan mataki a wannan Asabar ya ce alkalin alkalan zai gurfana a ranar Litinin a gaban wasu alkalai guda uku a birnin Abuja.
Sai dai bai bayar da cikakken bayani ba a game da takamaiman kadarorin da kotun da'ar ma'aikatan ke zargin alkalin alkalan da yin kwage kansu ba. Amma daga nata bangare fadar shugaban kasar ta Najeriya ta sanar da cewa kotun na zargin alkalin alkalan da boye wasu asusan ajiyar na banki da ke kunshe da makwadan kudade na Dalar Amirka da Euro da ma Pound.
A karkashin dokokin Najeriya dai ya zamo dole ga manyan jami'an gwamnatin kasar kan su bayyana illahirin kadarorin da suka mallaka kana ba su da izinin mallakar wani asusu na ajiyar kudin kasashen waje. Tuni ma dai gwamnatin Najeriyar ta bukaci alkalin alkalan da ya ajiye aikinsa.