1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gwamnati ta ce ta kusa kau da Boko Haram

Uwais Abubakar Idris/ASDecember 8, 2015

Hukumomi a Najeriya sun ce kokarinsu na murkushe kungiyar nan ta Boko Haram ya yi nisa ko da dai wasu 'yan kasar na tababa da wadannan kalamai na gwamnati.

https://p.dw.com/p/1HJOj
Nigeria Soldaten Offensive gegen Boko Haram
Hoto: Reuters/J. Penney

Gwamnatin Najeriyar ta bayyana wannan aniya ta kawar da Boko Haram din ne cikin wa'adin da ta ce ta baiwa sojojinta yayin wani jawabi ga manema labarai da ministan yada labarai na kasar Lai Mohammed ya yi a Abuja inda ya kara da cewar ''daga abin da muke da shi a kasa ina da karfin guiwa cewa nan da watan Disamba sojoji za su samu nasarar rage duk wani karfi na kungiyar Boko Haram ta yadda ba za su samu karfin kai hari yadda suke yi a baya ba. Kuma nasan an kakabe su daga wuraren da suke rike da su wanda ya lalata tsarin da suke da shi''

Von Boko Haram zurückgelassener Panzer in Yola, Adamawa, Nigeria
Sojin Najeriya sun ce suna cigaba da fatatakar 'yan Boko Haram daga inda suke.Hoto: picture alliance/AA/M. Elshamy

A daura da wannan kuma, duk da nasarar da ake ganin sojojin Najeriya na samu a zahiri wajen yaki da 'yan kungiyar ta Boko Haram da a lokutan baya ta rinka kame garuruwa a cikin kasar, rashin samun cikakken hadin kai daga wasu kasashen da Najeriyar ke kawance da su na zama babbar matsala kamar yadda gwamnatin ta nunar sai dai har zuwa yanzu mahukuntan Najeriyar sun ki ambata ko wace kasa ce bata bada hadin kan da ya dace, sai dai shaci fada da ake yi.

To sai dai duk da wannan, ministan ya ce ya kamata 'yan Najeriya fa su fahimci cewar yaki da ta'addanci abu ne da ke da sarkakiya don haka dole a dafa musu wajen cimma wannan kuduri da suka sanya a gaba da nudin ganin kungiyar ta kau baki daya. Batun fafutukar da wasu 'yan yankin kudu maso gabashin Najeriya ke yi na samun kasar Biafra ma dai na daga cikin irin batun da gwamnatin ta tabo, kasancewar wasu na cewar gwamnati ba ta tabuka komai ba kan wannan tada kayar baya sai dai ministan yada labaran na Najeriya ya musanta wannan zargi.

Boko Haram Kämpfer
Rikicin Boko Haram ya yi sanadin rasuwar dubban mutane da jawo asarar dukiya mai yawa.Hoto: picture alliance/AP Photo