1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Jam'iyyar APC ta lashe zaben gwamnan Ondo

October 11, 2020

Gwamna Rotimi Akeredolu na jam'iyyar APC ya lashe zaben gwamnan jihar Ondo da aka yi a karshen mako da kuri'u mafi rinjaye a gaban abokin takararsa na jam'iyyar adawa ta PDP Eyitaye Jagede.

https://p.dw.com/p/3jlUs
Nigeria Vizepräsident Yemi Osinbajo
Hoto: Novo Isioro

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta tabbatar da zaben gwamnan dan jam'iyyar APC biyo bayan ya samu kuri'u 292.830 a yayin da dan takarar jam'iyyar PDP ya samu 195.791. Haka kuma a zaben kananan hukumomi ma jam'iyyar da ke mulkin jihar Ondo wato APC, ta samu gagarumin rinjaye, inda daga cikin kananan hukumomi 18 jam'iyyar ta samu kananan hukumomi 15.

'Yan takara 16 ne dai suka shiga takara a zaben na gwamnan jihar, sai dai fafatawar ta fi tsanani ne tsakanin manyan jam'iyyun biyu na PDP mai adawa da APC mai mulkin kasar.

Sai dai duk da yabawa zaben da aka kammala cikin koshin lafiya kungiyoyin sa ido kan zaben sun koka da yadda aka yi amfani da kudi don jan ra'ayin masu zabe.