1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Fargabar samun ambaliyar ruwa a Najeriya

May 24, 2022

Masu rajin kare muhalli da masana gami da masharhanta sun fara mayar da martani kan wani sabon rahoton da Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya ta fitar, wanda ke nuna cewa za a samu ambaliyar ruwa a wasu jihohi.

https://p.dw.com/p/4Bnvt
Asarar Rayuka I Ambaliyar Ruwa I Najeriya
Asarar rayuka da matsugunai, sakamakon ambaliyar ruwa a NajeriyaHoto: dapd

A kusan kowane lokaci irin wannan hukumomi kan fitar da gargadi na yiwuwar samun ambaliyar ruwa a sassan Najeriya, domin a dauki matakan da su ka dace wajen magance matsalar ko kuma rage kaifin barnar da ambaliyar za ta yi. A wannan karon ma Hukumar Kula da Yanayin ruwan sama ta Najeriyar, ta fitar da rahoto da ke gargadin yiwuwar samun ambaliyar ruwan a kusan dukkanin jihohin kasar. Rahoton dai ya nunar da cewa kimanin kanan hukumomi 233 ne wannan matsalar ambaliyan ruwan za ta shafa, wanda kuma sun fito ne daga kowane bangare na Najeriyar. To sai dai masana da masu yaki da dumamar yanayi, na zargin cewa gwamnatoci da hukumomin da aka rataya musu hakkin daukar mataki kan irin wannan gargadi ba sa yin abin da ya kamata da a cewarsu ya sa wannan matsala ke kara fadada a kowace shekara.

Najeriya Kebbi | Ambaliyar Ruwa I Gonaki I Shinkafa
Ambaliyar ruwa dai, kan janyo asarar amfanin gona baya ga ta rayuka da kuma gidajeHoto: DW

#b#Abdullahi Muhammad Inuwa shi ne shugaban Kungiyar kare muhalli da ake kira da Movement for Restoration for Nature da Turancin Ingilishi, a cewarsa akwai babban aiki a gaban hukumomi in har su na son magance wannan matsalar ta ambaliyar ruwa. Sai dai akwai jihohi kamar Yobe da suka ce tuni sun dauki matakan da suka dace bayan samun gargadin, a cewar Dakta Muhammad Goje shugaban Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta jihar Yobe. Masu fashin baki kan harkokin yau da kullum dai na ganin matukar ba a dauki matakai na bai daya a dukkanin jihohin ba, akwai yiwuwar rayuwar mutane da dama ta fada cikin hadari kasancewar baya ga gidaje har gonaki matsalar ke shafa.