Najeriya : fargabar hare-hare a wuraren Ibada | Siyasa | DW | 07.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya : fargabar hare-hare a wuraren Ibada

Shugabannin addinai na kiran gwamnatin kasar, da ta kara kaimi wajen kawo karshen hare-haren da ke faruwa musamman a arewacin kasar.

Tsanantar kai hare-hare kan al'umma mabiya addinan Musulunci da Kirista a wuraren ibada, ko shakka babu abu ne da ke tayar da hankali a jihar Adamawa, lamarin kuma ya dada muni ne biyo bayan kisan sama da masallata 150 a jihar Borno da wasu mabiya addinin Kirista da ke ibada a Haikali a jihar Yobe da kuma wasu tagwayen hare-haren ranar Lahadin nan a birnin Jos da ma a wasu sannan arewacin Najeriya.

Sakamakon hakan ne ma, tuni shugabannin addinai ke sukar lamarin da kakkausar lafazi, inda shugaban kungiyar Izala ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau ke nuna rashin jin dadinsa musamman kan harin na garin Jos da ya shafi mambobinsa a wajen Tafsiri.

Nigeria Boko Haram Flüchtlinge Rückkehr ausgebrannter Panzer Michika

Wasu 'yan gudun hijira sun fara komawa gida.

Wani abin da ke zama abin daure kai cikin wannan lamarin na kashe-kashen na arewacin Najeriya dai shi ne, yadda tasirin jami'an tsaro ke komawa baya, musamman idan aka yi la'akari da yadda suka sami nasarorin makwanni shida gabanin zaben shugaban kasa da ya gabata. Yanzu dai akwai wadanda ke ra'ayin, gwamnati ta hada kai da shugabannin al'uma, masalan na addinai dama sarakunan gargajiya dama samun fahimta ta amana da jama'an tsaro don samun bayanan sirri.

Bishop Mike Moses, da ke jagorantar kungiyar mabiya addinin Krista ta kasa, reshen jihar Adamawa, na daga cikin masu bayyana wannan hanzarin. Da dama daga cikin masu nazarin al'amura dai na bayyana bukatar gwamnatin Najeriyar ta dubi yiwuwar amfani da matasan da ke da masaniyar wannan mummunar yanayi ta hanyar daukar su aikin masu kayan sarki, saboda wasu bayanan na cewa 'yan bindigan na farwa akasarin yankuna ne da suke da yakinin irin wadannan matasan ke ciki.


Sauti da bidiyo akan labarin