Najeriya: Dokar ta-baci kan tsaro | BATUTUWA | DW | 13.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Dokar ta-baci kan tsaro

Majalisar wakilan Najeriya ta nemi gwamnati ta sanya dokar ta-baci a yankin Arewa maso Gabashin kasar, domin kawo karshen hare-hare da ke haddasa asarar rayuka da ma dukiyoyi.

Bombenexplosion in Maiduguri Nordnigeria 2013

Boko Haram na ci gaba da cin karenta babu babbaka

Al'ummar yankin Arewa maso Gabashin Najeriya dai ba su yi maraba da wannan mataki ba. Batun na majalisar dai na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaron ke kara tabarbarewa a Najeriyar, inda koda cikin wannan makon ma kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram ta kai hare-hare da dama a yankin Arewa maso gabashin Najeriyar, abin da ya tilastawa shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari kai ziyara jihar Borno da ke zaman makyankyasar kungiyar Boko Haram din.

Haskensa ya fara dishewa?

To sai dai Shugaba Buharin bai samu tarbar arziki kamar yadda ya saba samu a jihar ba, inda har ma mazauna Maiduguri fadar gwamnatin jihar ta Borno su ka yi masa ihun "ba ma so". Tuni dai fadar gwamnatin Tarayyar Najeriya ta mayar da martani, inda ta ce wasu tsiraru ne da ba su da tarbiyya su ka yi wannan ihun, sai dai masu fashin baki da al'umma na ganin shugaban fa ya fara rasa farin jinin da ya ke da shi ne.

Nigeria Präsident Buhari

Farin jinin Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya na raguwa

Tun lokacin da Tarayyar Najeriya ta dawo kan tsarin mulkin demukuradiyya ba a samu wanda  ya samu farin jini a siyasa a jihohin arewacin Najeriya kamar Shugaba Muhammadu Buhari ba. Sai dai al'ummar Maiduguri sun nuna rashin gamsuwarsu ta hanyar yi masa ihun "ba ma yi",  abin da aka alakanta da yadda hare-haren mayakan Boko Haram ke kara ta'azzara. Ihun "ba ma yi" da aka yi wa Shugaba Buhari dai ya zama abin mamaki, ganin yadda aka yi masa ruwan kuri'u a zaben da ya gabata. Yayin da fadar gwamnatin Najeriyar ke nemen shafawa 'yan adawa kashin kaji kan ihun da aka yi wa shugaban kasar a Maiduguri, da yawa daga al'ummar yankin Arewa maso Gabashin kasar na ganin fara dawowa daga rakiyar shugaban ne.

Gwamna mai farin jini

Masu fashin baki kan al'amuran yau da kullum na ganin maimakon fadar gwamnatin ta tsaya zargin 'yan adawa ko wasu dangane da ihun da aka yi wa Shugaba Buhari a Maidugurin, kamata ya yi su nemi yadda za su gyara al'amura su kuma dawo da martabar shugaban da yanzu haka ake ganin yana rasa tagomashi. Rincabewar matsalar tsaron ce dai ta sanya majalisar wakilai ta nemi kafa dokar ta-bacin har sai an samu zaman lafiya, matakin da yawancin al'umma ba su yarda da shi ba ganin yadda gwamnan jihar Bornon Babagana Umara Zulum ya ke fafutukar kare al'umma daga halin da su ka shiga, a cewarsu mayar da shi gefe ya zama dan kallo da sunan dokar ta baci ba abin alkhairi ba ne.

Sauti da bidiyo akan labarin