Najeriya: Dokar kisa kan miyagun kalamai | Siyasa | DW | 01.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Dokar kisa kan miyagun kalamai

A Najeriya majalisar dattawa na aiki kan wani kudurin doka da zai tanadi hukuncin kisa ta hanyar ratayewa ga duk wanda aka samu da laifin furta kalamai na batanci da suka yi dalilin hada fitina da mutuwar jama’a.

Nigeria Präsident Muhamadu Buhari (Novo Isioro)

Shugabannin majalisun Najeriya tare da Shugaba Mahammadu Buhari da mataimakinsa

Damuwa a kan yawaitar furta kalamai na batanci ga takala da ke tunzura jama'a bisa bambanci na siyasa, ko kabilanci ne dai ya taso da wannan batu a yanzu. Domin sannu a hankali ana ganin karuwar lamarin a cikin kasar.

Sanata Aliyu Sabi Abdullah ne dai ya gabatar da kudurin da ke gaban majalisar. Kada kugen siyasa a Najeriya ya sanya samun karuwar lamarin da ke ta da hankali, wanda tuni hukumar wayar da kan jama'a ta yi kashedi, domin ta kai ga wasu na kiran za su yi zabe bisa addini. Abin da Hon Hussani Kangiwa ya bayyana damuwarsa a kai.

Wannan kuduri dai ya tanadi dauri na shekaru biyar, da tara ta Naira milyan biyar ga wanda ya furta kalaman batancin, sannan wanda laifinsa ya kai ga a yanke mishi hukuncin kisa za a yi masa hakan.

Abin jira a gani shine samun kasancewar hukudurin ya zama doka, da ma kafa hukuma ta musamman da ke cikin wannan tsari. 

 

Sauti da bidiyo akan labarin