1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damben gargajiya na kara samun karbuwa a Najeriya

Mouhamadou Awal Balarabe GAT
January 13, 2020

Shirin Labarin Wasannin na wannan mako ya duba batun damben gargajiya da gasar Afcon da kuma gasar ATP ta wasannin kwallon tennis da Sabiya ta lashe.

https://p.dw.com/p/3W8Lc
Nigeria Katsina Ringkampf
Hoto: DW/Y. Ibrahim Jargaba

Damben gargajiya a Najeriya:

A Tarrayyar Najeriya, damben gargajiya na kara samun karbuwa musamman arewacin kasar, inda matasa da dama suka dauki damben a matsayin sana'a, baya ga raya al'adar da aka gada daga kaka da kakkanni. 'Yan dambe kamar Su Garkuwan Chindo da Bahagon Shagon 'Yan Sanda da suka kama hanyar maye gurbin 'yan damben da suka yi suna a da irin su Shagon Mafara da dan dunawa. A yanzu ma dai a Jihohi da dama ne ake gudanar da wasan Damben a Nigeria, ciki har da katsina inda wakilinmu Yusuf Ibrahim ya je daya daga gidajen Dambe don gane wa idanunsu kuma ya jiye wa kunnuwansa yadda ake wasa 'yan damben. Kuna iya sauraren cikakken rahoton daga kasa a karshen rubutaccen labarin wasannin.

 

Shirye-shiryen gasar Afcon:

Shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Afirka Ahmad Ahmad da tawagarsa sun isa Kamaru domin tattaunawa da hukumomin kasar dangane da lokacin da ya fi dacewa a gudanar da gasar wannan nahiya cikin shekara mai kamawa. Bisa ga jadawalin da aka tsaida dai, a watan Yuni da Yuli ne ya kamata a shirya gasar AFCON ta 2021, amma akwai yiwuwar sake maida ta cikin watanni Janairu da Fabrairu kamar yadda aka saba a baya sakamakon ruwan sama da aka saba shatatawa a Kamaru a lokacin bazara. Wani dalilan da zai haddasa wannan canji shi ne gasar Kwallon Kafa ta kulob-kulob din kasashen duniya wacce aka shirya gudanarwa a watan Yuni da Yuli 2021. 

Tawagar ta CAF za ta yi amfani da wannan dama wajen gane wa idanunta inda aka kwana wajen shirya gasar kwallaon kafa ta Afirka ta 'yan wasa da ke bugawa a gida da za ta gudana a kasar Kamaru a cikin 'yan makonni masu zuwa. Kazalika manyan jami'an na Hukumar Kwallon Kafar Afirka za su san ko Kamaru ta shirya wajen daukar bakuncin kasan, wanda ya kamata ta shirya a 2019 amma jinkiri ya sa aka danka wa Masar. A ranar Laraba ne jami'a na kwallon kafar Afirka da hukumomin Kamaru za su sanar da shawarwarin hadin gwiwa da suka yanke dangane da lokacin gudanar da AFCON na 2012.

FIFA Ahmad Ahmad
Hoto: picture-alliance/dpa/Str

 

Gasar cin kofin zakarun Afirka:
Har yanzu dai muna fagen kwallon kafa a nahiyar Afirka, inda aka gudanar da mako na hudu na gasar kungiyoyin da ke rike da bajintar zakarun kasashensu wato Champions Lig. Tuni dai kungiyar Mazembe TP Mazembe ta Kwango da ta saba kai labari ta tsallake zuwa zagayen kwata fainal bayan nasarar da ta samu kan Primero de Agosto ta Angola da (2-1). Ita ma Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu ta kai bante zuwa zagaye kusa da kusa da na karshe sakamkon lallasa Usma Alger da ta yi da (2-1). Ita kuwa Esperance ta Tunisiya da ke rike da kofin zakarun Afirka tana bukatar yin canjaras ne kawai a daya daga cikin wasanni biyu da suka rage mata wajen cika burinta.

 

Gasar cin kofin kalubale ta Afirka:

A gasar cin kofin kalubale na Afirka wato Confederation Cup kuwa, Pyramid ta Alkahiran Masar, kungiyar da ta fi kowa kudi a gasar ta ci gaba da jan zarenta ba tare da ya tsinke mata ba, inda ta doke takwarata ta Masar El Masry da ci 2-0. Wannan dai shi ne karo na hudu da Pyramid ta samu nasara a wasanni hudu da ta buga, lamarin da ya sata  zama kungiyar farko da ta cancanci zuwa wasan kusa da na karshe na gasar Confederation Cup.

Ita ma Eyimba ta kudancin Najeriya ta gasa wa Paradou ta Aljeriya aya a hannu da ci 4-1, yayin da Zanaco ta Zambiya ta samu nasara a kan FC Asae ta Benin da ci uku da nema. Ita kuwa Motema Pembe ta Kwango Kinshasa ta yi wa Berkhane ci daya mai ban haushi.

 

 Gasar Super Cup ta Spain:
Yanzu kuma sai mu tsallaka nahiyar Turai, kuma za mu fara da kasar Spain, inda Real Madrid ta lashe kofin Super Cup a karo na 11 cikin tarihinta bayan mamaye Atletico Madrid ci 4-1 a bugun fenariti bayan mintina 120 na wasa ba tare da zura kwallo ba. Gwarzon wannan wasan da ya gudana a kasar Saudiyya Arabiya dai shi ne Thibaut Courtois: mai tsaron gidan Real dan Beljiyam wanda ya dakatar da kokarin Thomas Partey da Saúl Ñíguez a bugun daga kai sai mai tsraon gida. 
Godiya ta tabbata ga cochi Zinédine Zidane wanda karkashin horaswarsa Real Madrid ta lashe samu nasara a wasannin karshe 10 ya samu kofuna goma ciki shekaru hudu na baya-bayannan, kama daga bajintar zakarun Spain har i zuwa kofin zakaru na nahiyar Turai sau uku da kofin duniya na kulob-kulob din duniya sau biyu.

Saudi-Arabien Supercup-Finale - Real Madrid vs. Atletico Madrid
Hoto: picture-alliance/AP Photo/H. Ammar

 

Wasannin lig-lig na Turai:

A Ingila kuwa, bayan hutun lokacin sanyi, an koma fagen fama inda Liverpool ta samu nasara a kan Tottenham da ci daya mai ban haushi. Wannan dai shi ne nasara ta 20 cikin wasanni 21 a kakar wasa ta bana ga Liverpool, wacce a yanzu ke da maki 61. A yanzu dai Kungiyar Reds ta zarta Manchester City da maki 14, lamarin da ake ganin cewa da kamar wuya a ja ma wa 'yan wasa Jürgen Klopp birki a kokarin da take yi na neman bajintar zakarar lig ta Ingila na farko tun 1990.

Ita kuwa Manchester City ta yi Aston Villa dukan kawo wuka ci 6-1 , yayin da Manchester United ta samu galaba a kan Norwich  ci 4-0. 

A Italiya, Zlatan Ibrahimovic ya dawo Serie A da kafar dama, inda dan kasar Sweden din ya zira kwallo a karawar da AC Milan ta yi da Cagliari kuma ta doketa da ci 2-0. Ita kuwa Juventus Turin wacce ta doke As Roma da ci 2-1 ta haye saman teburi, bayan kunnen doki da Inter ta yi da Atalanta 1-1. A matsayi na uku kuwa, Lazio ce ta sami wannan dama bayan doke Naples da ci 1-0.

A lig din kasar Faransa kuwa, an yi karon batta tsakanin Paris Saint Germain da Monaco, inda  bayan da Neymar ya zira kwallon farko, Monoca ta farke ta kuma kara kafin a rama wa kura aniyarta. A karshe dai PSG da Monaco sun tashi wasa ci 3-3 ko ta'ina. A yanzu dai Paris Saint Germain ce ta kasance a saman teburin lig din Faransa, kuma ta yi wa Olympic da Marseille ratar biyar duk da cewa Marseille ta samu nasara da ci 1-0 a gaban Rennes.

 

Australien | ATP Cup in Sydney |  Serbien | Novak Djokovic
Hoto: Getty Images/M. King

Gasar kwallon Tennis ta ATP:
Kasar Sabiya wacce dan wasanta Novak Djokovic ke a matsayi na biyu a fagen Tennis na duniya ta lashe kofin farko na gasar ATP, bayan da ta doke Spain da ci 2-1 ranar Lahadi a birnin Sydney.
Duk da cewa an doke Serbia da ci 1-0  a wasa tsakanin masu matsayi na biyu tsakanin Dusan Lajovic da Roberto Bautista , Amma Novak Djokovic bai yi wata-wata wajen doke rafel nadal (6-2, 7-6) don daidaita tsakanin kungiyoyin biyu ba. Daga bisani ne Djokovic da Viktor Troicki suka doke 'yan spain da  6-3, 6-4. Wannan ne ya sa Spain ta kasa lashe kofin ta biyu a jere bayan Kofin Davis da ta ci a cikin Nuwamba 2019 a Madrid.