Najeriya da Iraki suka fi fuskantar matsalar ta′addanci | Zamantakewa | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Najeriya da Iraki suka fi fuskantar matsalar ta'addanci

Cibiyar nazarin tattalin arziki da zaman lafiya a kasashen duniya ta wallafa wannan rahoton, inda ta ce mace-mace ta hanyar ta'addanci ya karu da kashi 80 cikin 100 a shekara ta 2014.

Yawan mutanen da suka rasu ta hanyar ta'addanci ya dada karuwa a duniya. Hakan ya fito ne a cikin wani sakamakon rahoton da cibiyar kula da tattalin arziki da tsaro ta "Institute for Economics and Peace" mai cibiyoyi a kasar Amirika, ta fitar a wannan Talata inda ta ce yawan mutanen da aka kashe a shekarar da ta gabata ta 2014 ya karu ne da kashi 80 cikin 100 idan aka kwatanta shi da na shekarar da ta gabata ta 2013.

A sakamakon da aka bayar na ta'addanci a duniya, a kalla mutane 32.658 ne aka kashe sakamakon hare-haren ta'addanci a shekara ta 2014, wanda idan aka kwatanta da na shekara ta 2013 wanda alkalumma suka nunar cewa an hallaka mutane 18.111 ta hanyar ta'addanci a duniya, wadannan alkaluma dai su ne suka fi daukan hankalin wannan cibiya kamar yadda darektanta Steve Killelea ya yi wa DW bayani.

IS Kolonne Fahrzeuge Toyota

Kashi 44 na mace-macen Iraki da Siriya fararen Hula ne

"Nazarin wannan shekara ya nuna karuwar mutuwar mutane ta sakamakon ayyukan ta'addanci da kashi 80 cikin 100"

Hanyoyin da kungiyar ke gudanar da bincike

Binciken ya nunar cewa ayyukan ta'addancin ya fi kamari ne a cikin kasashe biyar cikinsu har da Najeriya. To ko ta yaya wannan cibiya ke tattara iri-irin wadannan bayannai Steve Killelea shi ne babban darektan wannan cibiya mai kula da tattalin arziki da tsaro.

"Muna tattara alkalumman ta'addanci ne wadanda aka samar daga jami'ar Maryland ta nan Amirka tunda nan ne ake tattara duk wasu alkalumma mafi yawa kan abun da ya shafi ayyukan ta'addanci shi ne muke yin nazari a kai."

Alkaluman binciken sun nunar cewa kashi 51 cikin 100 na kashe-kashen da aka yi a shekarar da ta gabata sun faru ne daga kungiyar Boko Haram da kuma IS, sannan kuma binciken ya nunar cewa kashi 78 cikin 100 na mutanen da aka kashe, da kuma kashi 57 cikin 100 na hare-haren da aka kai, sun kasance ne a cikin kasashe biyar da suka hada da Afghanistan, Iraki, Najeriya, Pakistan da kuma Siriya. Kasar Iraki ta fi fuskantar matsalar ta'addancin inda aka samu akalla mutane 9.929 da suka rasu ta hanyar harin ta'addanci, abun da ke nuni da munin lamarin.

Karuwar hare-haren ta'addanci a Najeriya

Nigeria - Soldaten an der Grenze zu Niger

Kasashe biyar cikinsu har da Najeriya ke kan gaba

Najeriya ma dai ta fuskanci karuwar tashe-tashen hankulla na 'yan ta'adda inda binciken ya nunar cewa an kashe a kalla mutane 7.512 sakamakon harin ta'addanci a shekara ta 2014 wanda hakan ya nunar cewa an samu karuwar mace-macen da kashi 300 cikin 100 idan aka kwatantashi da na shekarar 2013. Sai dai duk da haka akwai banbancin yadda ake mayar da hankali kan lamarin idan aka kwatanta da harin da aka kai a birnin Paris na Faransa inda kan haka Seidik Abba dan jarida kuma editan shafin nan na sadarwa na Mondafrique mai cibiya a birnin Paris na Faransa ya yi tsokaci.

Binciken dai ya nunar yadda mace-macen mutane ya karu a cikin kasashen da ba kasafai ake samun hare-haren ta'addancin ba kamar su Australiya, Beljiyam, Canada da Faransa inda yawan wadanda suka rasun ya karu daga mutane 59 a shekara ta 2013 zuwa 67 a 2014.

Masu binciken dai sun sanar cewa, akasarin dalillan da ke haddasa ayyukan ta'addancin da ake samu a cikin wasu kasashen, sun dauko tushe ne daga rikicin siyasa, ko wani rikici na cikin gida da ake samu a wasu kasashen da kuma matsalar cin hanci ko wasu al'ammurra na rishin kwatanta gaskiya da adalci daga magabata.

Sauti da bidiyo akan labarin