Najeriya cikin shekara mai wucewa | Siyasa | DW | 27.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya cikin shekara mai wucewa

An shafe tsawon shekarar da ke karewa tare da kokarin cika buri na siyasa maimakon alkawuran zabukan da ke tsakanin mahukunta da talakawan da ke kasar.

Za a iya cewa ta dai shigo cikin fatan sauyi an mata kasafin kudi na sauyin ga kasa, to sai dai kuma tana shirin karewa a cikin rikici na siyasa ga shekara ta 2013 mai karewa da daga dukkan alamu ke zaman ta baya ga dangi a cikin tasiri.

Duk da cewar dai ya kai ga gargadi dama tsorata kowa da nufin hana furta batun tsaida takararsa a zabukan da ke tafe, ba'a kai ga ko ina ba dai al'ammura suka fara saki a cikin fadar gwamnatin kasar da ta zauna ta kalli 'yan kore da masu adawa cin karensu babu babbaka a kokari na zarce sa'a wajen burge 'yan kasa.

Abun kuma sannu a hankali ya rikide daga fata na gani a zahiri a bangaren talakawan da suka dauki lokaci suna neman sauyi tare da komawa ga fage na fama na siyasa da rikicin na tsaron da ya adabbi talakawa ya hana su kansu sarakunan kasar rawar gaban hantsin dake zaman al'ada a garesu.

An dai ga kungiyar gwamnonin PDP a karon farko an kuma hango rabuwa a tsakanin daukacin gwamnonin kasar ta Najeriya gida biyu, kafun daga baya aka kai ga haihuwar 'yan bakwan da suka rikide ya zuwa 'yan biyar sukai wa PDP sakiyar da ba ruwa.

Abun kuma da daga dukkan alamu ya kama hanyar tada hankulan kusan kowa a kasar da a cewar Ibrahim Shehu Shema da ke zaman gwamnan Jihar Katsina sannan kuma jigo a cikin rikicin ke kama da cin amanar al'umma.

Koma dai ya zuwa yaushe ne son zuciyar yake shirin kawa domin kyale cika alkawarin na zabukan na shekara ta 2011 dai, daga alamu shekarar tana shirin karewa tare da babbar asara na shirin zuwa wurin talakawan da suka jajirce suka sha rana wajen tabbatar da masu mulkin da ke rikicin neman iko.

An dai kare shekarar tare da kusan rabin lokutan gwamnonin kasar dai na tsakanin jihohi da Abuja da ke zaman sabuwar matattarar rikicin, sannan kuma shi kansa hankalin shugaban kasar Goodluck Jonathan ya fi karkata zuwa warware rigigngimun na siyasa maimakon cika alkawarinsa da al'ummar kasar ta Najeriya. Abun kuma da a cewar Salisu Dasuki Nakande da ke zaman tsohon minista na gwamantin kasar yanzu haka kuma jigo a tsakanin masu adawar kasar ke da ruwa da tsaki da son zuciyar mazaunan fadar gwamnatin kasar na Abuja.

Raba kai don son mulki ko kuma gaza hakuri da sabbabbi na sauye sauye dai, ga Dr Babagoni Imam da ke zaman wani masani na siyasa, 'yan siyasar kasar ta Najeriya na fakewa ne a cikin jahilcin talakawa wajen son ran da rashin adalcin a cikin harkokin mulkin da kyautata rayuwar mutane.

Abun jira a gani dai na zaman tasiri na sabuwar shekarar da ke kamawa ga rayuwar mutane a cikin kasar da annobar ta shugabanci ke zaman gubar da ke kara mamaye rayukan mahukunta a matakai daban-daban.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin