1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cece ku ce kan 'yan matan Dapchi

February 26, 2018

Gwamnatin Najeriya ta ce kimanin 'yan matan sakandaren Dapchi guda 110 ne su ka bace a yayin da gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam ya daura laifin sace ‘yan matan kan janye sojoji da aka yi.

https://p.dw.com/p/2tMZ0
Nigeria Mädchenschule in Dapchi
Hoto: DW/A. Kriesch

A jawabin da gwamnatin Najeriya ta yi ta bakin Ministan yada labarai Lai Mohammed, ya sanar da cewa bayan tantance alkaluman dalibai da suka koma makaranta bayan harin, kimanin dalibai dari da goma ne ba‘a samu labarin inda su ke ba a halin yanzu.
Gwamnatin ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen ganin an ceto wadannan dalibai duk da cewa ba yanke hukuncin cewa mayakan Boko Haram ne su ka sace daliban a wani hari da ake zarginsu da kai wa a ranar Litinin da ta gabata ba.


Jinkirin fitar da alkaluman sunayen wadan dalibai da kuma ci gaba da dagewa da gwamnatocin ke yi na kin yarda da cewa Boko Haram ce ta sace wadannan mata, ya kara tayar da hankulan iyaye da su suka cewa suna da cikakkun hujjoji. Malam Bashir Manzo shi ne shugaban kungiyar Iyayen da aka sace ‘ya ‘yansu a makarantar sakandaren ‘yan mata da ke  garin Dapchi mai nisan kilomita dari daga Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe.


Gwamnan jihar Yobe Alh Ibrahim Gidam ya daura alhakin harin kann matakin nan na  janye sojoji da aka yi daga garin da ya bai wa mayakan damar shiga dama sace 'yan matan, ya bayar da kwatanta lamarin da wanda ya auku a garin Buni Yadi wanda shi ma bayan janye sojoji aka kai hari kuma aka halaka dalibai da dama. Iyaye da ‘yan uwan ‘yan matan sun nuna bacin rai da kuma halin da suka shiga na tashin hankali, a dalilin  kwan gaba kwan baya da ake samu musamman daga bangaren gwamnatin jihar Yobe wace a baya ta fitar da bayanai ma su karo da juna kan bacewar  ‘yan matan da kuma zargin janye Sojojin da zama sanadiyar sace yaran.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani