Karbe kudaden asusun da aka dade ba a yi amfani da su
July 25, 2024A Najeriya matakin da babban bankin kasar ya dauka na umartar dukkanin bankunan kasar su aika masa da kudadden da ke a asusun da aka dade ba'a yi amfani da su ba a tsawon shekaru 10 zuwa sama domin shi ya janyo martni a kan amfani ko akasin hakan.
An dade ana yamadidi a kan batun karbar wadannan kudade da ke a asusun bankunan da ba'a amfani da su kafin lamarin ya tabbata a yanzu, inda babban bankin Najeriya ya bada umurni kai tsaye ga bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudade cewa duk kudin da ke wani asusu na banki da ka kwashe shekaru 10 ko fiye da haka ba'a yi amfani da su ba to bankunan su aika wa babban bankin da daukacin kudin a wani kebantacen asusu da bankin ya bude. Kudade ne dai masu yawan gaske da ake hasashen bankin zai samu sama da Naira tirliyan 20, domin Najeriyar na da irin wadannan asusun da suka kai sama da milyan 72 da ake da kudade dankare a cikinsu. Wannan dai sabon abu ne da ba'a saba da shi ba a kasar. Mallam Umar Yakubu shine shugaba wata cibiyar yaki da cin hanci da rashawa da ke Abuja.
To sai dai ga Mallam Abubakar Ali Masani ne a fanin tattalina arziki a Najeriya da yankin Afrika ta Yamma na ganin akwai kokarin tsaftace kuaden da aka jibge a irin wannan asusu kamar yadda babban bankin ya bayyana.
A sanarawar da daraktan manufofin tafiyar da harkokin kudi na babban bankin Najeriyar John Onoja ya sanya wa hannu ya bayyana cewa akwai yiwuwar bankin zai sayi takardu masu daraja domin adanawa masu wadannan kudade. Tun a 2014 ne dai aka ga karuwar irin wadannan asusun banki tun bayan da aka bullo da tilasta duk mai asusun banki sai ya yi rijista ta lambar tantanacewa don gane masu ajiye a bankuna inda mutum guda kan bude asusu barkatai. Babban bankin Najeriya ya bayyana zargin aikata zambar kudade ta wadannan asusun.
Wannan sanarwa dai ta zaburar da masu irin wannan asusu ko dai su bayyana don fara amfani da su ko kuma su sa ido abinda zai tabbatar da hallacin kudadden da ke ciki da aka kwashe shekaru da dama ba tare da amfani da su ba.