1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin karamar Sallah a Najeriya

May 13, 2021

A Najeriya al'ummar Musulmi sun gudanar da bukukuwan karamar sallah a hukumance, kamar yadda mai alfarma sarkin Musulmi ya umarta a duk fadin kasar, bayan cika azumi 30.

https://p.dw.com/p/3tLnQ
Nigeria Abuja Sultan  Sokoto
Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar na III, na NajeriyaHoto: DW/N. Mahaman Kanta

Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar da kuma gwamnan jihar Sakkwato Aminu  Wazirin Tambuwal da sauran mahukuntan jiha suka sallaci tasu sallar. Mutane da dama ne dai suka halarci wannan sallah ta bana a masallatan idi dabam-dabam, kasancewar sallar bara ba a samu halarta ba sakamakon annobar cutar coronavirus.

Jawaban sarkin Musulmi da gwamna da suka saba gabatarwa, a wannan lokacin sun mayar da hankali kan muhimmancin samar da tsaro da kuma kara daukar matakan kiyaye kamuwa da cutar corona. Shagulgula dai sun kaure a sassan Najeriyar, inda a jihar Sakkwato masu dawaki da rukuma ke ta yin kara-kaina a titunan birnin, a kokarin raya al'ada da aka saba ta kai gaisuwar ban girma a fadar Sarkin Musulmi a irin wannan lokaci. Sallar dai ta bana ta samu halartar dimbin mutane da aka dauki dogon lokaci  ba'a ga irin sa ba anan Sakkwato.