1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Bude hanyar Maduguri zuwa Gamboru

Al-Amin Suleimane Mohammad/GATJuly 7, 2016

Rundunar sojojn Najeriya ta bude hanyar da ta tashi daga Maiduguri zuwa Dikwa da Gamboru bayan da hanyar ta kasance a rufe shekaru da dama sakamakon rikicin Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1JLDe
Nigeria Soldaten in Damboa
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Tun a shekara ta 2013 ne dai aka rufe wannan hanyar, bayan da hare-haren mayakan Boko Haram suka tsananta inda ta kai sun karbe iko da yawancin garuruwan yankin, sai a wannan lokaci ne aka bude hanyar domin amfanin jamaa da kuma jamian tsaro.


Rundunar sojojin karkashin jagorancin babban hafsan sojojin kasa Laftanar Janar Tukur Buratai da gwamnan jihar Borno Kashin Shetima ne suka yi kwarya-kwaryar bikin bude hanyar a ranar Laraba inda suka bi ta tare da motocin jigilar fasinjoji. Wannan hanyar wace ta tashi daga Maiduguri zuwa mafa zuwa Dikwa zuwa Gamborun Ngala ta kasance mai matukar muhimmanci saboda yadda ta hade Najeriya da kasashen Kamaru da Chadi da ma Afirka ta Tsakiya.
Kakakin rundunar Sojojin Najeriya Kanar Sani Usman Kuka sheka ya tabbatar min da fara amafni da wannan hanyar a tattaunawarsu da wakilin DW a Gombe ta wayar tarho.

Nigeria Armee Task Force gegen Islamisten Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP


Masu fashin baki kamar Bala Jungudo Gombe sun yi imanin cewa bude wannan hanya babbar nasarar ce ga kokarin wanzar da zaman lafiya inda suka bukaci hukumomi su tabbatar da biyan sojojin hakokinsu a kan lokaci don karfafa musu gwiwa.

Shugaban kungiyoyin direbobi na NURTW Malam Ahmad Musa ya bayyana muhimmancin wannan hanya inda ya kuma bada tabbacin jigilar fasinja a kai-a kai.
Sai dai mutanen da suka yi murna da bude hanyar sun kuma nemi a dauki matakin magance karbar kudi da jamian tsaro ke yi a irin wadannan hanyoyi don samun nasar yin aikinsu. Wannan ya sa Abdullahi Muhammad Inuwa shugaban Kungiyar Kare dan Adam da Muhalli yin kira ga hukumomi da su bincika masu karbar kudin daga hannun fasinjojin don hukunta masu yin hakan da nufin magance matsalar.

Straßenszene in Maiduguri
Hoto: picture-alliance/AP Photo