1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Boko Haram ta halaka sojoji 15

Ramatu Garba Baba
August 10, 2018

Akalla sojoji 15 da wani jami'in hukumar agaji ne suka halaka a sakamakon wani harin kwantar bauna da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a garin Damasak da ke a jihar Borno.

https://p.dw.com/p/32wZp
Nigeria Kampf gegen Boko Haram | ARCHIV
Hoto: picture alliance /AP Photo/L. Oyekanmi

Wani jami'in hukumar agajin gaggawa na NEMA da ya nemi a sakaye sunansa, ya bayar da labarin yadda mayakan suka bude wuta da bindigogi kan sojojin da jami'in na su guda a yayin da suke tsakiyar aikin katange wani yanki a garin na Damasak. Harin na ranar Larabar da ta gabata ya kasance hari mafi muni a jihar da ta rasa mutum fiye da dubu talatin a sanadiyar ayyukan ta'addanci. 

Mayakan na Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare nan da can duk kuwa da kokarin da hukumomin kasar ke yi don ganin an dakile ayyukansu da kuma tabbatar da tsaro a yankin gabanin babban zaben kasar.