Najeriya: Bada tallafin kudi ga gwamnatocin jihohi | BATUTUWA | DW | 13.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Bada tallafin kudi ga gwamnatocin jihohi

Fiye da kudi Naira miliyan dubu dari biyar da ashirin da biyu ne gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bai wa jihohin kasar domin samun zarafin biyan maikatansu albashi da kuma gudanar da ayyukan raya kasa.

Daga cikin adadin kudi Naira miliyan dubu 522 da miliyan 74 da aka samu daga biyan bashin fiye da kima na Paris Club da London tare da wasu cibiyoyin kudi na ketare, an rabar wa jihohin Najeriya 35 ne kudaden baki daya.

Kashim Shettima Gouverneur Bono Nigeria (DW/U. Shehu)

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima

Bincike ya nunar cewar kowace jiha da irin abin da ta samu daga wannan adadin kudi, inda wasu jihohi kamar su Lagos, Bayelsa, Kaduna, Rivers da wasun su saka sami fiye da Naira miliyan dubu 14, wasu jihohi kuwa irin su Benue da Bauchi, sun sami fiye da Naira miliyan dubu 11 yayin da jihohi irin su Filato da Nasarawa kuwa sun sami fiye da Naira miliyan dubu 8 ne daga kudin na Paris Club.

Wasu jihohi irin su Benue da Bauchi, rahotanni sun nunar cewar gwamnatocin jihohin na kokarin ganin sun sauke wannan nauyi na albashi amma jihohi kamar su Eketi bincike ya nuna har yanzu lamarin bai canza zani ba, inda ma'aikatan jihar suka karbi albashin wata guda kachal daga cikin kudi naira miliyan takwas da milyan 877 da aka basu. Don haka Shugaba Buhari cikin jawabin sa na karshen shekara ya yi wa gwamnatocin jihohi gargadi kan wannan kudi.

Nigeria Parlamentspräsident Aminu Tambuwal (picture alliance/Photoshot)

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal

Yanzu abin jira a gani shi ne yadda gwamnatocin jihohin kasar za su sarrafa kudaden da aka basu ta hanyar da ta kamata, kasancewar gwamnatin Tarayya ta lashi takobin sa ido wajen ganin ba'a ci gaba da watanda da dukiyoyin jama'a ba kamar yadda aka saba a baya.

 

Sauti da bidiyo akan labarin