Najeriya ba ta bukatar dakarun Majalisar Dinkin Duniya | Labarai | DW | 17.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ba ta bukatar dakarun Majalisar Dinkin Duniya

Shugaba Jonathan ya nunar da cewa da tallafin dakarun sojojin Kamaru da Nijar da Chadi dakarun kasarsa sun karbe mafi yawan garuruwan da kungiyar ta kwata a baya.

Shugaba Goodluck Jonatahan na Najeriya ya bayyana wa Majalisar Dinkin Duniya a jiya Alhamis cewa kasarsa ba ta bukatar tallafin dakarun kasa da kasa na Majalisar a yakin da take yi da kungiyar Boko Haram.

Shugaban mai barin gado ya bayyana cewa bukatar da tafi muhimmanci daga bangaren na Majalisar Dinkin Duniya, na zama ta bada tallafi wajen ganin an sake ginawa da bada taimako ga yankunan al'umma da ayyukan ta'addancin kungiyar ya daidaita sakamakon ayyukansu na tsawon shekaru shida.

Shugaban ya bayyana haka ne bayan ganawa da mazanni na musamman daga sakataren na Majalisar Dinkin Duniya wadanda ke wakilitarsa a tsakiya da yammacin Afrika, wato Mohammed Ibn Chambas and Abdoulaye Bathily.

A jawabin shugaba Jonathan ya nunar da cewa da tallafin dakarun sojan kasar Kamaru da Nijar da Chadi dakarun kasar sun karbe mafi yawa garuruwan da kungiyar ta kwata a baya. 

A cewar cibiyar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar kimaninn mutane miliyan daya da dubu dari biyar ne rikicin na Boko Haram ya raba da muhallnasu a arewacin na Najeriya, yayin da kuma fiye da mutane 13,000 suka hallaka.