1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sauya salo a garkuwa da mutane

Abdullahi Maidawa Kurgwi YB
April 5, 2019

A Najeriya masana harkokin tsaro sun kawo shawara kan matakai da suka kamata hukumomi su dauka wajen magance matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa. Masu garkuwa da mutane a sabon salo na shiga gidajen jama'a.

https://p.dw.com/p/3GNHu
Polizei in Nigeria
Jami'an tsaro kan tsare mutane bisa zargi ko da ba mai lefi baHoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

To yanzu dai kusan kowane wayewar gari sai an sami labarin yadda ake garkuwa da jama'a don neman kudin fansa, inda kafin wannan lokaci jama'a kan ji tsaron yin balaguro kan wasu manyan hanyoyin kasar kamar hanyar Abuja zuwa Kaduna, ko  Keffi zuwa Akwanga, da ma wasu hanyoyin da ake yawaita yin garkuwa da jama'a, to sai dai yanzu abin ya zarce manyan hanyoyi zuwa gidajen jama'a.

Mista Audu Joseph wani mai sharhi ne kan al'amuran tsaro a Najeriya, ya ce a tsakiyar makon nan masu garkuwan sun shiga har gidan wani dan'uwansa, suka yi garkuwa da shi kuma yanzu haka suna kan tautaunawa kan  batun kudin fansar.

Polizei in Nigeria
Hoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

To sai dai masharhanta irin su Sani Abdul na kallon lamarin karuwar garkuwa da mutane musamman a yankin arewacin Najerya kan wasu dalilai kamar yadda za ka ga mutane ma'aikatan gwamnati na hidima da ta fi karfin samunsu da sauransu, yanzu haka dai masu garkuwan kan yi anfani ne da wasu dabaru suna shiga gidajen jama'a, inda su kan yi garkuwa da wani daga cikin iyali ciki har da yara kanana don meman a biya kudin fansa.

To sai da wasu ‘yan Najeriya na dora laifin karuwar lamarin kan hukumomin tsaro da kuma gwamnatin kasar. 

Yanzu haka dai wannan matsala ta garkuwa da jama'a na neman ta gagari kundila, don haka masharhanta ke gani cewar muddin baa dakile ta ba yanzu, to zuwa gaba, lamarin zai zarce  jama'a masu karamin karfi zuwa manyan-manyan mutane da ke tsakanin al'ummar kasa.