1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan sanda sun mutu a yayin artabun yin garkuwa da Turawa

Ramatu Garba Baba
April 27, 2019

Kakakin 'yan sandan jihar Rivers ya ce an sace ma'aikatan kamfanin hakar mai na Shell guda biyu tare da halaka wasu 'yan sanda da ke aikin tsaronsu, lamarin ya auku ne a ranar Juma'ar da ta gabata inji jami'in.

https://p.dw.com/p/3HXrs
Nigeria Ölplattform vor der Küste
Hoto: AP

Lamarin dai ya auku ne a yayin da suke kan hanyarsu ta koma wa gida jiya Juma'a,  daga yankin da suke aikin hakar mai a jahar Rivers da ke a kudancin Najeriyan. Kawo yanzu, ba a kai ga baiyana asalin kasashen da mutanen da aka sacen suka fito ba tukun na. Yankin dama ya yi kaurin suna wajen sace mutane musanmanTurawa don neman kudin fansa.