1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An samu tashin hankali a Jos

Gazali Abdou Tasawa
September 30, 2018

A Najeriya an fuskanci tashin hankali a wannan Lahadi a garin Jos, inda aka yi asarar rayuka. Sai dai tuni gwamnati ta dauki matakai tare da bai wa mazauna unguwannin da rikicin ya afku umurnin zama a cikin gidajensu.

https://p.dw.com/p/35l0P
Nigeria - Bombenanschlag in Jos
Hoto: Getty Images

A Najeriya an fuskanci tashin hankali a wannan Lahadi a garin Jos, inda aka yi asarar rayuka. Kodashike dai babu alkaluma a hukumance da ke nuna adadin mutane da suka rasa rayukansu a lokacin tashin hankalin, to amma wakilinmu na jihar Filato Abdullahi Maidawa Kurgwi, ya ce rikicin ya fi kamari ne a wasu unguwanni da ke birnin Jos, da suka hada da Unguwan Damisa, Dutse Uku, Tina Junction, Rikkos, Bauchi Junction, Unguwan Rukuba da kuma Farar gada.

Komishinan 'yan sandan jihar Filato Udie Udie, cikin wata sanarwa ya bukaci al'ummomi da ke da zama a unguwanin da aka sami tashin hankali, da su kasance cikin gidajensu, sakamakon yanayin da aka shiga. Komishinan watsa labarai na jihar Filato Yakubu Datti, ya ce gwamnatin jiha tare da jami'an tsaro sun hada kai wajen daukan matakan shawo kan sabon rikicin na Jos....

Wakilin mu yace anyi hasarar rayuka da dukiyoyi lokacin sabon rikicin wanda ya faro tun a safiyar Juma'a inda kuma yau Lahadi aka kuma fuskantar wani rikicin.