Najeriya: An sake yin garkuwa da dalibai | Labarai | DW | 17.06.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: An sake yin garkuwa da dalibai

Wasu yan ta'adda da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da dalibai mata a jihar Kebbi.

'Yan bingiga sun sake yin awon gaba da yara mata yan makaranta da ba a tantance adadinsu ba kawo yanzu a wata kwalejin gwamnatin tarayya da ke garin Yauri na jihar Kebbi arewa maso yammacin Najeriya, kwanaki kalilan bayan sace wasu daliban a garin Kwantagora mai makwabtaka da birnin na Yauri.

Gabanin sace yan makarantar da malamansu guda uku, sai da yan bindigar suka hallaka wani jami'in dan sanda daya yayin da su ke musayar wuta da barayin ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Nafiu Abubakar.

Haka zalika a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin kasar ma masu garkuwa da mutane sun dauke wasu 'yan China hudu ma'aikatan layin dogo bayan hallaka jami'in dan sandan da ke gadinsu.